Tinubu zai ziyarci Katsina
Tinubu zai ƙaddamar da wasu ayyukan Gwamna Umar Dikko Radda
Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai ziyarci Jihar Katsina.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Zango, ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce shugaban zai kai ziyarar ce, domin ƙaddamarwa da kuma rangadin wasu ayyukan da Gwamna Umar Dikko Radda ya aiwatar a jihar.
- Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
- Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
Karin bayani na tafe.