Tir da mujallar Charlie Hebdo!

Addini shi ne hanyar rayuwa bisa hana bautar wani abun bautawa in ba Allah ba, ta hanyar amfani da tsare-tsaren da wannan abin bautar ko kuma makusantansa suka tanadar domin tafi da rayuwar yau da kullum bisa wasu tanade-tanade ko tsare-tsare.  Addini ya rabu gida daban-daban, kamar yadda masana addini su ka yi bincike kuma […]

Tir da mujallar Charlie Hebdo!
Tir da mujallar Charlie Hebdo!

Addini shi ne hanyar rayuwa bisa hana bautar wani abun bautawa in ba Allah ba, ta hanyar amfani da tsare-tsaren da wannan abin bautar ko kuma makusantansa suka tanadar domin tafi da rayuwar yau da kullum bisa wasu tanade-tanade ko tsare-tsare. 

Addini ya rabu gida daban-daban, kamar yadda masana addini su ka yi bincike kuma su ka tabbatar, wanda a tsarin bauta kowa na da ‘yancin yin addininsa, ba tare da cin zarafi ba, kuma a ka’ida bai kyatatuwa ga mabiya addinai cin dunduniya ko aibata wani ko wasu ginshikai na wani addinin daban.
Misali, addinin Musulunci wanda ya bukaci bawa ya mika wuya kacokan ga Allah Ubangijin halittu, da kuma yin imani da manzon Allah Annabi Muhammad (Tsira da aminci su tabbata a gare shi) da kuma kafatan Annabawa da manzannin Allah. Haka kuma Musulunci ya haramta zalunci akan kowa ba kadai sai iya mabiya addinin ba, ba ya halatta ga musulmi na kwarai ya cutar da wani ko wasu al’ummar da ba sa bin addinin ballantana kuma mabiya addinin bai daya, yin hakan ka iya jawo fushin ubangiji, saboda irin zaman lafiya da masalahar da ke cike a cikin addinin Musulunci. Hakazalika a addinin Kiristanci da Yahudanci, tanade-tanaden addinan tun asali ba su bada damar suka ko cusguna wa wasu mabiya addinan da suka sha bamban da na su ba.
Zance na gaskiya, addinin Musulunci ya koyar da yin da’a da biyayya da kuma yarda da dukkan Annabawa da mursalan da Allah (SWT) ya aiko su, tun daga Annabi Adam (AS) har zuwa cikamakonsu, kuma jagoransu Annabi Muhammad (SAW), wanda rashin yin imani da su ka iya ruguza Imanin dan Adam.
Tun a shekarun baya a yankin Turai ake samun wasu tsagerun mutane da suka himmatu wajen cin zarafin musulmi, ta hanyar rubutu ko zanen mutum mutumin don yin izgili ga Annabin Allah, saboda kawai a kuntata wa Musulunci da Musulmi, wai su na ikirarin ‘yanci ne na Magana, ko kuma ‘yancin ’yan jarida ya bada wannan damar. Ai wayewa ba hauka ba ce, kuma wannan lamarin duniya ta san cewar ana aiwatar da shi ne don a tura wa mabiya addinin Musulunci haushi.
Duk da suna batun ‘yanci to ai har da ‘yancin gudanar da addini ga jama’a a fadin duniya. Duk da sanin rashin dacewar abin, amma jagoranci duniya bai daukar wani kwakkwaran mataki, ganin yadda abin ke tada hankulan mabiya addinin Musulunci.
To wai me ake nufi da Musulmin duniya? Na farko dai ina dalilin yin wannan batancin? Shin takalar fada ake yi ko kuwa so ake yi a nuna wa duniya Musulunci ba a bakin komai yake ba?
Kamar yadda na fada a farko babu addinin da ya aminta a ci zarafin wasu masu bin wani addinin daban, to in haka ne, me zai sa shugabannin irin wadannan sakarkarun mutanen ba za su ja musu kunne ba; su kuma nuna rashin a mincewarsu karara? Ni kam na yi imanin Musulmin kwarai ba zai taba munzata wani ko wasu don kawai suna da bambancin addini, kai ko da kuwa hakan ta faru, to za ka ji malaman Muslunci sun fito sun soki abin. Kodayake kalilan daga mabiya addinin Kiristanci sun yi tur da ayyukan batancin, sai dai tun a shekarun baya da hakan ta faru a kasar Denmark har ila yau abin kara bayyana yake, kuma wannan shi ne dalilin da ya tunzura wasu matasa daukar hukuncin a hannunsu.
Duk da yake daukar hukunci ko doka a hannu ya saba da ka’idar Musulunci, amma bai kamata a bar dukan jaki a koma taiki ba. Da tun farko an dauki matakin hana su yin irin wannan tabargazar, to da hakan ba ta faru ba. Don kuwa a gaskiyar lamari babu addinin da zai saka ido ana masa cin kashi haka, kuma na yi imanin ban da Musulmi suna da hakuri da tuni fitinar ta girmama.
Da haka nake tur da wannan cin zarafin Manzon Allah(SAW) da mujallar Charlie Hebdo, da ma sauran kafafen da ke aikata irin wannan badakalar. Ina kuma jawo hankulan ‘yan uwa Musulmi da su ci gaba da addu’ar Allah wadai su kuma yi tur da nuna damuwarsu karara.
Sannan shugabannin Musulmi su hada kawunansu su rika magana da murya daya tak, don kawar da ire-iren wadannan cin zarafin da izgilanci da gangan. Dole ne Musulmi su kyamaci wannan badakalar, su kuma sanya babbar alamar dakatarwa da za ta hana cin zarafin al’ummarsu da addininsu da kuma uwa uba Annabinsu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi).
Allah ka kara wa Annabi daraja, wasila da fadila ameen.

Mudassir ya rubuto ne daga NTA Zariya kuma za a iya samunsa a adireshin imel dinsa kamar haka: [email protected]

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi