Tirela ta halaka ‘yar sanda da wani mutum a Gombe
An gargaɗi direbobi da su riƙa bin dokokin tuƙi da kuma kula da lafiyar motocinsu domin kauce wa irin wannan iftila’i.
Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a yankin Sabuwar Mile 3 da ke kan hanyar Gombe zuwa Yola ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, ciki har da wata jami’ar ’yan sanda, tare da jikkatar wasu da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, lokacin da wata babbar mota ƙirar DAF wadda ke ɗauke da buhunan hatsi, ta yi hatsari ta kuma kutsa cikin babura uku, masu tafiya a ƙasa da kuma wasu shaguna da ke gefen hanya.
- Sabon Masallacin Fadar Zazzau ya sake ruftowa ana tsaka da aiki
- Manyan ’yan takara 3 sun ƙi amincewa da zaɓen fidda gwanin APC a Kaduna
Binciken farko da rundunar ’yan sanda ta gudanar ya nuna cewa direban motar ya yi yunƙurin shiga hanyar da ba ta dace ba inda ya yi aron hannu kuma birkin motarsa ya shanye.
A sanadiyar hatsarin ne wata jami’ar ‘yan sanda mai suna Sharifa Gaina ta rasu nan take, haka kuma wani mutum da ba a tantance sunansa ba shi ma ya mutu a wurin.
Wasu mutane da dama, ciki har da direban motar, sun samu raunuka daban-daban waɗanda a halin yanzu suna karɓar kulawa a asibiti.
Haka kuma hatsarin ya haddasa lalacewar babura uku da kuma asarar kayayyaki a shagunan da abin ya shafa.
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya tayar da hankalin jama’a, yayin da jami’an ceto da ‘yan sanda suka garzaya wurin domin kai ɗauki da kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya jajanta tare da yin kira ga direbobi da su riƙa bin dokokin tuƙi da kuma kula da lafiyar motocinsu domin kauce wa irin wannan iftila’i.
Ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin hatsarin tare da ɗaukar matakan kiyaye aukuwar hakan a gaba.
Shi ma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah Ya jikansu.