Tirela ta hallaka ’yan acaba uku a Keffi
Akalla ’yan acaba uku ne wata tirela ta hallaka a ranar Talatar da ta gabata a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa lokacin da ta rasa birki ta buge su a wani shataletale kafin ta fada a wani gini.Wani dan acaba mai suna Kabiru dalhatu da lamarin ya auku a gabansa ya ce, “Ranar Talata […]
Akalla ’yan acaba uku ne wata tirela ta hallaka a ranar Talatar da ta gabata a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa lokacin da ta rasa birki ta buge su a wani shataletale kafin ta fada a wani gini.
Wani dan acaba mai suna Kabiru dalhatu da lamarin ya auku a gabansa ya ce, “Ranar Talata da misalin karfe 7:30 na dare ina tsaye a shataletalen gidan mai na Total sai na ga tirelar ta kwararo a guje a gangara, kuma na ji ana cewa ku tashi babu birki, ku tashi babu birki. Nan take na kauce, ina kallon abin da ke faruwa. Lokacin akwai wasu ’yan acaba da suka tsaya a shataletalen don motoci su wuce, haka babbar motar nan ta zo ta murkushe su.” Ya ce koda yake bai san adadin mutanen ba, amma ya ga mutum uku. Kuma ya ce da ya zo washegari da safe sai ya tarar da gawar wani abokin acabarsa mai suna Bashir dansakkwato, mai kimanin shekara 30 da ke zaune a Unguwar Sabon Layi a garin Keffi ba a fitar da babur dinsa daga karkashin motar ba.
Tirelar mai lambar Filato G 428 JJN da rubutan YA DAFI’U a jikinta, da ke shake da duwatsu wanda babu wanda zai iya ba da cikakken bayani kan dalilin rashin birkin nata, domin direba da yaran motar sun gudu sun bar motar tun kafin ta fadi, kuma har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto babu wanda ya san inda suka shiga.
A ranar Laraba, jami’an Hukumar Kare Hadurra ta kasa sun je da babbar katafila don janyo motar, amma tun misalin karfe 10:00 na safe har zuwa karfe 4:00 na yamma ba su samu nasara ba, balle a san abin da ke karkashin ta. Shugaban Hukumar FRSC shiyyar Keffi Mista Jacob Inyima ya tabbatar da aukuwar hadarin inda ya jajanta wa iyalan mamatan, tare da kira ga gwamnati ta dubi lamarin wannan wuri mai yawan jawo hadurra.