Tirela ta kashe mutum 6 wasu 15 sun ji rauni A Gombe

Mutane 6 sun mutu wasu 15 suka ji raunuka a wani hatsarin da wata tirela ta yi a hanyar Abacha Raod da ke unguwar Jekadafari a garin Gombe.

Tirela ta kashe mutum 6 wasu 15 sun ji rauni A Gombe

Tirelar raken da ta yi hatsari a Babbar Hanyar Kubwa da ke Abuja

Mutane 6 sun mutu wasu 15 suka ji raunuka a wani hatsarin da wata tirela ta yi a hanyar Abacha Raod da ke unguwar Jekadafari a garin Gombe.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa a jihar Gombe, Felix Theman ne ya tabbatar da hakan a yammacin ranar Juma’a.

Ya ce tirelar tana dauke ne da shanu 27 da wasu yara a saman bodin ta.

Ya ce hanyar ta yi kadan wa manyan motoci su bi, amma masu tireloli suna kaunar bin ta, duk da cewa tana da kwane-kwane.

Ya ce irin Yyran da suke hawan saman bodin motar sune suke yin ihu suna zuga direbobin su kuma suke kara gudu a cikin gari saboda burgewa da hakan ya kai su ga hatsari.

Daga nan sai ya ce za sun yi zama da masu ruwa da tsaki a harkar tukin manyan motoci dan jan kunnen direbobin tirelar da mafi yawan lokaci suke bai wa yaran motarsu suke ganganci a cikin gari domin kiyaye yawan aukuwar hatsari.

Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’

BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato

Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC