Tirela ta makarɗe mutum 2 har lahira a titin Abuja-Keffi
Hatsarin ya auku ne a ranar Talata a kan hanyar Mararaba.
An tabbatar da mutuwar wasu mutum biyu tare da jikkatar wasu da dama, yayin da wata tirela ta bi ta kan wasu motoci biyar a hanyar Abuja zuwa Keffi.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata.
Wasu ganau, sun ce direban tirela ne ya bi ta kan wasu motoci bayan da birki ya tsinke masa a hanyar Mararaba.
Wata majiyar kuma ta ce mutum huɗu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Aminiya ba ta tabbatar da adadin waɗanda suka rasu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Sai dai Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a babban birnin tarayya, Chorrie Isah Muta’a, ta shaida wa Aminiya cewa kawo yanzu mutum biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu.
“Mutane biyu ne suka mutu a hatsarin, wanda ya faru kimanin sa’o’i biyu da suka wuce (da misalin ƙarfe 4 na yammacin jiya). Birkin tirelar ne ya tsinke, wanda ya sa direban ya gaza shawo kanta. Ya bi ta kan wasu motoci biyar, ɗaya daga cikinsu ta yi kaca-kaca, inda fasinjoji biyu da ke cikinta suka rasu,” a cewar Muta’a.
Kwamandan ta ce an tura jami’an hukumar zuwa wajen da hatsarin ya auku domin kula da ababen hawa.