Tirela ta murƙushe ɗaliba har lahira a Bauchi
Makarantar ta tabbatar da rasuwar ɗalibar.
![Tirela ta murƙushe ɗaliba har lahira a Bauchi Tirela ta murƙushe ɗaliba har lahira a Bauchi](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/Federal_Polytechnic_Bauchi_Main_Gate-scaled.jpg)
Wata ɗalibar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Faith Aluko Adesola, ta rasa ranta bayan da wata babbar mota ta murƙushe ta.
Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Alhaji Rabi’u Muhammad ne, ya tabbatar da faruwar lamarin.
- Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025
- Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas
Ya ce Adesola ɗaliba ce da ke ajin farko (ND1) a Sashen Koyon Aikin Jarida na makarantar.
A cewarsa, tana kan ɗan acaba domin zuwa makaranta lokacin da babbar motar ta yi awon gaba da babur ɗin a kusa da kofar shiga makarantar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta.
“Da muka samu labarin, tawagar makaranta da suka haɗa da shugaban tsaro da shugaban kula da harkokin ɗalibai sun garzaya wajen, amma likitan makaranta ya tabbatar da rasuwarta,” in ji Muhammad.
Direban babur ɗin ya tsira da ransa a hatsarin.
Makarantar ta sanar da iyayenta, kuma wakilanta sun halarci jana’izarta a ranar Alhamis.
Muhammad, ya ja hankalin ɗalibai da su kasance masu taka-tsantsan yayin ƙetare hanya domin gujewa irin wannan hatsari.