Tirela ta murƙushe mutane a Gadar Hotoro a Kano

Ana fargabar mutane da dama sun rasu bayan wata tirela ta murƙushe su a Gasar Muhammadu Buhari da ke yankin Hotoro a a Jihar Kano.

Tirela ta murƙushe mutane a Gadar Hotoro a Kano

Ana fargabar mutane da dama sun rasu bayan wata tirela ta murƙushe su a Gadar Muhammadu Buhari da ke yankin Hotoro a Jihar Kano.

Tirelar ta kife ne bayan da ta kwace a ƙarƙashin gadar, a hanyarta ta zuwa Kudancin Najeriya daga Yankin Arewa maso Gabas.

Wani ganau ya bayyana cewa kimanin mutane 20 da kaya ne ke cikin motar a lokacin da ta kife, inda wasu daga cikinsu suka rasu suka jikkata.

Shi ma wani ganau mai suna Shu’aibu Hamisu, ya ce tirelar ta fito ne daga hanyar Maiduguri tana kokarin sauya hanya zuwa titin Zariya Road, amma ta kwace wa direbanta.

Hadari irin haka dai ya sha aukuwa a karkashin gadar a kimanin shekara guda da ta gabata, inda aka yi asarar rayuka da dama.

Yawancin motocin da hakan ke faruwa da su suna dauke ne kayan abinci da dabbobi da mutane da kayan gwangwan daga yankin Arewa zuwa yankin Kudu.

Yawancin masu gudanar da harkokin a yankin sun alakanta aukuwar hadura a gadar da gudun wuce sa’a da manyan motocin ke zuwa da shi, inda suke yi karo a karshe.

Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi

’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike

Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno