Tirela ta murƙushe wani mutum a Neja
Tuƙin ganganci da gudun wuce sa’a ne ya janyo aukuwar haɗarin tirelar wadda ta taso daga Bida zuwa Kutigi.
Wani mutum da aka bayyana da suna Yanma wanda ya fito daga yankin Masaba na Ƙaramar Hukumar Bida ta Jihar Neja, ya gamu da ajalinsa bayan wata tirela ta murƙushe shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daidai Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Bida da tsakar ranar Laraba.
- ‘Lokacin kawo ƙarshen haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya ya yi’
- Ba mu janye daga zanga-zangar da za a gudanar ba — NLC
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa reshen Jihar Neja, Kumar Tsukwam ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa tuƙin ganganci da gudun wuce sa’a ne sanadiyyar aukuwar haɗarin tirelar wadda ta taso daga Bida zuwa Kutigi.
Ya ce tuni an miƙa wa ’yan uwan waɗanda haɗarin ya shafa gawarsa yayin da ake ci gaba da bincike.