Tirelar da jami’an Kwastam ke kokarin kamawa ta danne mutum 4 a Kwara

Jami’an dai na kokarin kama motar ne bisa zarginta da fasakwaurin shinkafa.

Tirelar da jami’an Kwastam ke kokarin kamawa ta danne mutum 4 a Kwara

Wata tirela dauke da kaya da ake kyautata zaton jami’an Hukumar Hana Fasakwauri ta Kwastam ke kokarin kamawa, ta danne wata mata da ’ya’yanta hudu a birnin Ilorin na Jihar Kwara.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Talata.

Hakan na zuwa ne kusan wata daya bayan wasu fusatattun matasa sun yi taho-mu-gama da jami’an hukumar da ke kokarin kama wani direban tirela da ake zargin ya dauko haramtattun kaya a Ilorin.

Aminiya ta gano cewa lamarin, wanda ya faru a dab da shatale-talen garejin Offa, ya haddasa kazamin cunkoson ababen hawa na tsawon sa’o’i.

Rahotanni dai sun ce ’yan sanda sun tarwatsa wasu dandazon matasan yankin da ke kokarin ba hammata iska da jami’an na Kwastam.

Ko da yake ba a samu asarar rai ba, wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa matar, wacce ke tuka wata mota kirar Mitsubishi, ta ji mummunan rauni tare da daya daga cikin ’ya’yan nata.

Yanzu haka dai su biyu na can suna samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.

A cewar ganau din, “Bayan faruwar lamarin, tirelar ta danne motar wacce matar da ’ya’yan nata ke ciki tsawon mintuna kafin a kawo musu dauki.

“Jami’an Kwastam ne ke bin motar, bisa zargin tana dauke da shinkafar da aka yi fasa-kwaurinta. Amma bayan ta fadi, sai aka gano katako ne ma a cikinta,” inji majiyar.

Sai dai Kakakin Hukumar ta Kwastam a Jihar, Chado Zakari, ya musanta cewa dakarunsa ne ke bin motar, inda ya ce kawai kashin kaji ake neman shafa musu.