Tirelar kayan gwari ta yi sanadin mutuwar wani matashi
Wani matashi mai suna Salisu Kura, dan kimanin shekaru 30 da ke sana’a a kasuwar Ilefo, inda ake sayar da kayan abinci a Jihar Legas, ya rasa ransa yayin da tirelar da ke makare da kayan gwari ta danne shi.Lamarin, wanda ya auku a makon da ya gabata, ya jefa mutanen kasuwar cikin alhini da […]

Wani matashi mai suna Salisu Kura, dan kimanin shekaru 30 da ke sana’a a kasuwar Ilefo, inda ake sayar da kayan abinci a Jihar Legas, ya rasa ransa yayin da tirelar da ke makare da kayan gwari ta danne shi.
Lamarin, wanda ya auku a makon da ya gabata, ya jefa mutanen kasuwar cikin alhini da fargaba don nan take ya mutu har sai da aka kawo mota mai kugiya ta daga tirelar sannan aka jawo gawar mamacin duk kayan cikinsa a waje.
Shugaban kasuwar, Alhaji Ado Shu’aibu ya ce lamarin ya girgiza jama’a.
“Wata mota dauke da kaya ta makale a cikin wani rami, sai aka kira shi Salisu don ya samo musu jak na daga mota, kasancewar yana da alaka da direbobin kasuwar. Ana cikin daga motar, sai shi da wani suka shiga karkashi don taimakawa, sai motar ta zame daga jikin jak din ta danne su, amma Allah da ikonSa, daya yaron ya fito da kyar da rauni a kunne. Shi kuwa nan take ya mutu saboda raunin da ya yi, domin sai da aka nemo mota mai kugiya ta janye motar, sannan aka fito da gawarsa aka kai wurin ajiyar gawarwaki na asibitin gwamnati”. Inji shi.
Mutane da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana Salisu a matsayin mutum mai hakuri da rikon amana.
Malam Shafi’u ya ce, “Salisu yaro ne mai hakuri kuma ba shi da hayaniya, mai ladabi da biyayya ga manya da kuma na kasa da shi”.