Tireloli 60 dauke da kayan agaji sun yi layar zana a Borno
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce tireloli 60 daga cikin 113 dauke da kayayyakin abinci da Gwamnatin Tarayya ta tura Jihar Borno don raba wa ’yan gudun hijirar Boko Haram sun yi layar zana.Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin kai kayan a tireloli 113 domin saukaka matsalolin […]
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce tireloli 60 daga cikin 113 dauke da kayayyakin abinci da Gwamnatin Tarayya ta tura Jihar Borno don raba wa ’yan gudun hijirar Boko Haram sun yi layar zana.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin kai kayan a tireloli 113 domin saukaka matsalolin abinci lokacin da ya samu labarin ’yan gudun hijirar na cikin tasku. Sanata Ndume ya ce “A kan haka na zo Maiduguri don duba yadda za a raba kayan, kuma kafin in zo da kusan mako daya mun san motocin su riga yiwo gaba, kuma na samu bayanin sun iso Maiduguri, amma da na je don duba motocin kafin mu fara rabon, abin bakin ciki sai na ga motoci 53? Kuma ban samu amsa kan inda saura motoci 60 suka yi ba, kuma har yanzu ban ji daga bakin dan kwangilar ba, sai dai na samu labarin cewa Hukumar EFCC, ta kama shi yanzu haka yana hannunta.”
Sanata Ndume ya ce ba za su raba kayan abinci ba sai sun gano sauran motoci 60, kuma zai koma ya yi wa Shugaban kasa bayani domin ya san halin da ake ciki, “Ba za mu lamunci karkatar da hakkin mutane ba, an wuce zamanin cin hakkin mutane balle na ’yan gudun hijira. Don haka gwamnati ba za ta lamunci wannan mugun hali ba,” inji shi. Ya ce ’yan gudun hijirar suna bukatar tallafi sosai, don haka wani mara tausayi mai neman azurta kansa ta kowace hanya ya nuna rashin tausayi ga mutanen ba abin da za a lamunta ba ne.