Tiren-taliyar Maman-tine
A watannin da suka arce ’yan makarantarmu na da masaniya cewar ’Yan sisi ta umarci daukacin kamfanonin cilla batutuwa a cikin kurtu na halo-alalo su dade layukan kurtun maganar duk wanda ya ki yin rajistar layinsa/ta. Kai ta kai ga sai da na koka ganin yadda aka toshe wa Dodanniya matar Dodo kurtunta, amma aka […]
A watannin da suka arce ’yan makarantarmu na da masaniya cewar ’Yan sisi ta umarci daukacin kamfanonin cilla batutuwa a cikin kurtu na halo-alalo su dade layukan kurtun maganar duk wanda ya ki yin rajistar layinsa/ta. Kai ta kai ga sai da na koka ganin yadda aka toshe wa Dodanniya matar Dodo kurtunta, amma aka kyale Hajiya Kanusiyya, matar Gizo-gizon-dakin gwaggo ta yi ta yin batunta. Sai ga shi yau dara ta ci gida, domin ’Yan sisi ta kakaba wa Maman-tine tarar Hauro tiren-taliya sili da gashin balama dari tsayuwa bisa kafa daya.
dimbin Haurobiyawa ne suka shiga cikin damuwa, don gudun kada a toshe musu kafar kurtun yin batu a layin likon alakar Maman-tine, musamman jin cewa akwai tarar Hauro tiren-taliya sili da gashin balama dari tsayuwa bisa kafa daya da Hukumar ’Yan sisi ta kakaba musu. Kusan kowa yasan yadda wannan kamfanin layin batu a cdikin kurtun Magana na Kudancin Ifrikiyya ya sha jefa al’umma cikin tsomomuwa. A wasu lokutan kana cikin batu sai kawai a katse maka layi; idan mutum bai yi sa’a ba, daga nan layin kurtunsa ya fara laulayi. Ko kuma idan hukumar gudanarwar Kamfanin Maman-tine na son yin cukudi-cukudi, wato sabuwar hanyar cin kudi, sai kawai ta yi walankewa da masu ta’ammali da layinta, ta jefa mutum cikin tsarin tallata haja, ta yadda kusan kowane wata sai an zare wa mutum zaren Hauro.
Haurobiyawa ku sani ana aiko mini da batutuwa game da wasannin tamolar casawa da lallasawa da Aron-salala da Jibirin-tus da Madarar kwallo. Sannan wannan kamfani ya saba cillo mini batu kan cutar mazarkwailla, amma fa ba suga rawar ingarma ba. Kuma wani abu da kamfanin Maman-tine bai sani ba, ni a sashen watsattsake da buda wagagen littattafai na Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya nike yin kwadagion neman kadago, amma duk da haka sai su riga cillo mini kanun labarai, shi ma idan wa’adinsa ya karkare sai a sake sabon zubin janye wuri da zimmar barina da na-mujiya wuri-wuri.
Kai haslai ma da na shigo wurin kwadago na iske man-kaza na bayan kango yana korafi kan yadda Kamfanin Maman-tine ke sabunta masa kidan nisantar da abokan yin batu a cikin kurtu. Kuma shi babban tkaicinsa, shi ne, wai bai san yadda aka yi ya kutsa kai cikin wannan tsari ba. Duk da cewa, nasan wannan kamfani ya tafka wa GizBaba ta’asa a kwanon tasa, ina son jefa azargagiyar zargin cewa, ‘sun san yana dan taba harkar nanaye.’ Irin su GizBaba idan an cillo musu jijjigar jita da jaujen jajen masu garaya ko kidan ganga da bushe-bushen sarewa, ta yi wu ana son su dan rausaya ne. Hujja a kan haka, ’yan makaranta kun san kirarin da na yi wa man-kaza na bayan Katanga, wato:
“GizBaba in ji Nigawa,
Namijin majigin Haurobiyawa,
Yaro abokin Indiyawa,
Da Michael Jackson mawakin Amurkawa,
Nufina na bayan kango mai rausayawa.”
Batu na ingarman karfen karafa, idan Maman-tine ba ta shiga tyaitayinta ba, to duk zan umarci ’yan makarantata su koma cikin gwalalo, su rika yi wa jama’a gwalo, suna cewa, “Halo, alalo, siddabarun dabara salo-salo, amma da zarar layin yin batunsunsu ya jirkice, sai su ce jalli-jogar janjalo! Idan kuma na ga dama sai in jefa su cikin kurtun Iya-talle, dama ita hawainiyar kurtun magana ce da ta sha rikida da lakabi iri-iri. Badon-fanni da Ikon-nane-titi hart a wilkita, ta wilkita ta zama Iya-talle.
Don kada a dauka ko ina adawa da Maman-tine ne, a’a, ko kadan ba haka lamarin yake ba. Lallai a duba shafin bayanai kan mashakatar lilo da tsallake-tsallaken sadarwart na’ura mai kwakwalwa da cikin Jaridar Dalilin-taron-su, ta ranar karamin lauje da mnadambaci na shekarar dubu karamin lauje da sili da babban lauje, za a ga tsokacin Haurobiyawa gamke da tarar Hauro tiren-taliya da gashin balama dari tsayuwa bisa kfa daya da ’Yasisi ta kakaba wa Maman-tine. Mafi yawan masu ce ce-ku ce sun caccaki Maman-tine, tare da sukar lamirinta kan yadda ta dode musu layin batu, ko kuma zare musu zaren Hauro a lokuta mabambanta
’Yan sisi dai tana tuhumar Maman-tine da cinikin layuka malala gashin tunkiya babban lauje, wadanda ba su da rajista, tunda doka ta yanke wa’adin toshe layuka a cikin watan kwankwadar nakwadin wannan shekara.
Matukar ba a baje na-mujiya a kan Maman-tine ba, tabbas za ta iya tsuwurwuta wasu dabarun da za ta mayar na kwadi cikin kwakware, ta yadda ba za ta ji ciwon wannan tara ba. Kuma wasu ma na iya kwaikwayonta, ta yadda za su samu dammar musguna wa Haurobiyawa masu ta’ammali da kurtun magana na halo alalo.
A nan zan karkare batutuwan darasin wannan mako tare da bijiro da bukatar a dan yi karin wannan tara, sannan a tabbatar sun jinka wa hukuma damin Hauronta, don a samu yi wa talakawa aikace-aikacen raya kasa. Sannan a ja musu na-zomo kan lallai su daina jefa masu ta’ammali da Kurtun magana cikin tsirfar tsare-tsaren tallata hajar da ba su suka nema ba. Haurobiyawa mu tursasa kowa ya bi ka’ida, don mu samu fa’ida.