Tirka-tirka tsakanin Super Eagles da hukumomin Libya
A yanzu dai CAF ta gabatar da batun ga kwamitin ladabtarwarta domin bincike tare da ɗauƙar mataki kan wanda ya karya dokar hukumar.
Tuni dai Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta sanar da cewa ta samu bayanai kan abin da yake faruwa tsakanin hukumomin ƙwallon ƙafa na Nijeriya da Libya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin ƙasashen nahiyar ta 2025.
CAF ta ce ta tuntuɓi hukumomin ƙwallon ƙafar ƙasashen Najeriya da na Libya domin jin abin da ya faruw game da yadda tawagar Super Eagles ta maƙale a filin jirgin saman Abraƙ da ke Libya na sa’o’i masu yawa, bayan nan aka ce su sauka.
A yanzu dai CAF ta gabatar da batun ga kwamitin ladabtarwarta domin bincike tare da ɗauƙar mataki kan wanda ya karya dokar hukumar.
Ba za mu buga wasa da Libya ba — Super Eagles
Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya – Super Eagles, William Troost-Ekong ya ce shi da sauran ’yan wasan sun yanke shawarar cewa ba za su buga wasa da Libya ba a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka ta 2025.
Troost-Ekong ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya bayyana ɓacin ransa kan halin da suka tsinci kansu bayan isarsu Libya domin buga wasan da aka tsara karawa ranar Talata.
’Yan wasa da jami’an tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles sun tsinci kansu cikin wani yanayi bayan da suka shafe sama da awa 16 a filin jirgin sama na Abraƙ da ke Libya.
A yammacin ranar Lahadi ne, tawagar Super Eagles ta isa Libya domin buga zagaye na biyu na wasan neman shiga gasar kofin ƙasashen Afirka ta 2025 da za a yi a Morocco.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Libya suka tilasta jirgin Super Eagles sauka a filin jirgin sama na Abraƙ, maimakon filin jirgin saman Benghazi da tun asali aka tsara ’yan wasan za su sauka, kamar yadda hukumar kwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayyana.
A wasan farko da aka buga a Najeriya, Super Eagles ɗin ce ta doke Libya da ci ɗaya da nema.
Hotuna da bidiyo da NFF ta fitar a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ’yan wasan na Super Eagles suka yi zaman dirshan a filin jirgin saman, inda suke ta hira bayan shafe fiye da sa’o’i 12 cikin jirgi daga Nijeriya zuwa Libya.
Hukumomi sun ce bayan nan, ’yan wasan kuma za su sake saɓar titi inda za su yi tafiyar awa uku a mota daga Abraƙ zuwa Benghazi wurin da za su taka leda.
Ramuwar Gayya ko kuskure?
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya ma ta yi ƙorafi kan yadda ta ce hukumomin Nijeriya suka ajiye su tsawon sa’o’i lokacin da jirginsu ya sauka a Nijeriyar a wasan farko da suka zo yi.
Wani abu da ke ci gaba da ɗaure wa mutane kai a shafukan sada zumunta shi ne ko abin da ya faru ramuwar gayya ce da hukumomin Libya suka ɗauka a kan abin da suka ce ya faru da su a Nijeriya? Bincike ne zai bayyana gaskiya!
Sai dai hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya (LFF) ta ce ba da gangan aka bar tawagar Super Eagles ta Nijeriya yashe a filin jirgi ba, duk da cewa su ma an yi musu hakan a Najeriyar.
“Mun damu matuƙa kan abin da ya faru da tawagar ƙwallon ƙafan Nijeriya, gabanin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Afirka,” in ji sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.
“Duk da dai mun yi nadamar abin da ya faru, muna kuma jan hankali cewa irin wannan matsala tana iya faruwa bisa kuskure a kowane lokaci, ko dai saboda ’yan gyare-gyare a filin jirgi ko saboda binciken jami’an tsaro ko kuma wasu ƙalubale na daban daga jiragen saman ƙasa da ƙasa.
‘’Muna matuƙar mutunta Nijeriya, kuma muna bayar da tabbacin cewa ba da gangan aka samu wannan matsala ta karkatar da jirgin tawagar Super Eagles ba.
“Mu ma mun fuskanci irin wannan matsala lokacin da muka je Nijeriya a makon da ya gabata, amma ba mu zargi hukumomi da aikata hakan da gangan ba.”
Bayan wasan farko da Nijeriya ta doke Libya 1-0 a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a, an tsara buga wasa na biyu a birnin Benghazi na Libya ranar Talata.
Libya za ta shigar da Super Eagles ƙara
Hukumar ƙwallon ƙafar Libyan ta yi tir da matakin da NFF ta ɗauka na fasa buga wasa na biyu na neman gurbibn gasar cin kofin nahiyar Afrika.
Ta yi ƙorafin hukumomin Nijeriya ba su nuna musu dattaku ba a wasan da suka yi a Nijeriya, tare da cewa halin da ‘yan wasan Nijeriya suka shiga bai kai kwatankwacin wanda ’yan wasanta suka shiga ba a Nijeriyar a makon jiya.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ɗauki alwashin shigar da ƙarar Super Eagles kan matakin da ta ɗauka na komawa ƙasarta da fasa buga wasan.
Ta ce Nijeriya ta je ta saɓa wa magoya bayanta da suka shirya kallon wasan da aka tsara yi ranar Talata, hakan ya sa ta bai wa magoya bayan Libya haƙuri cikin sanarwar.
Sai dai hukumomin Nijeriya sun musanta dukkanin zargezargen da humumar ƙwallon ƙafa ta Libyan ta yi.
Ta ce ita aka hana duk wata dama da ’yanci da take da shi kama daga ’yanci fita su kama otel da na yawo da na cin abinci.
A daren Talata hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya ta wallafa hotunan ’yan wasanta a filin atisaye, tana cewa hakan wani ɓangare ne na shirin tunkarar wasan Nijeriya a ranar Talata.
Yayin da ita kuma tawagar Super Eagles ta koma Nijeriya, bayan yanke hukuncin da ta yi na fasa buga wasan.
CAF ta ce ta tuntuɓi hukumomin ƙwallon ƙafar ƙasashen Nijeriya da na Libya domin jin abin da ya faruwa game da yadda tawagar Super Eagles ta maƙale a filin jirgin sama da ke Libya awanni masu yawa, bayan nan aka ce su sauka.
Me matuƙin jirgin ya ce?
Matukin jirgin ɗan ƙasar Tunisiya da ya tashi da tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya zuwa Libya ya yi ƙarin haske kan al’amuran da suka kai ga karkatar da su ba zato ba tsammani zuwa wani filin jirgin sama mai nisa, Al-Abraƙ, maimakon inda suka nufa birnin Benghazi.
An tura jirgin zuwa Al-Abraƙ, wani ƙaramin filin jirgin sama da aka saba amfani da shi wajen gudanar da aikin hajji, mai tazarar kilomita kusan 300 daga gabashin Benghazi.
A cikin wata hira ta faifan bidiyo da ɗar jarida Pooja Media ta watsa a Ɗ (Twitter a baya), matuƙin jirgin ya bayyana cewa karkatar da lamarin ba shi ne shawararsa ba amma hukumomin Libya ne suka umarta.
“Shirin jirgin ya sauka ne a birnin Benghazi na yankin Benina, kuma mun samu amincewa daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasar Libya.
“Amma yayin da muka fara gangarowa, an umurce mu da mu karkata zuwa birnin Al-Abraƙ, wanda ba haka ba ne. Har ma da aka tsara a
madadin filin jirgin saman. Wannan shawarar ta fito ne daga manyan hukumomin Libya, ba ni ba.”
Ya nuna damuwarsa kan haɗarin da ke tattare da rashin tsaro da sauyin bagtatan ke tattare da shi, inda ya bayyana cewa an ƙididdige man da ke cikin jirgin domin inda aka nufa.
“A sufurin jiragen sama, muna lissafin man fetur ne bisa ga inda muka nufa, karkatar da kai ba zato ba tsammani na iya kawo cikas ga tsaro. Na sha tambayar umarnin kuma na yi musu gargaɗi game da adadin man jirgin, amma sun dage cewa mu sauka a Al-Abraƙ, bisa umarnin hukuma.” in ji shi.
Sannan ya ƙaryata ikirarin da kafafen yaɗa labarai suka yi cewa karkatar da jirgin shi ne zaɓinsa, yana mai jaddada cewa an rubuta dukkan hanyoyin sadarwa na jiragen sama kuma ana iya bayar da su a matsayin shaida.
“An rubuta komai. Na nemi sauka a Benghazi kamar yadda tsarin jirgina ya tanada, amma sun musanta hakan, inda suka umarce ni da in karkatar da jirgin nan take. Yanayin Al-Abraƙ ya haifar da ƙarin ƙalubale,” in ji shi.
Matuƙin jirgin ya bayyana ƙaramin filin jirgin a matsayin wanda ba shi da kayan aiki, ba shi da muhimman tsarin kewayawa kamar Instrument Landing System (ILS) da VHF Omnidirectional Range (VOR), wanda zai sa a iya yi sauka da daddare ko cikin yanayi mai wuya na musamman.