Tolulope: Ya kamata a binciki mutuwarta
‘Yar uwar mace ta farko mai tuka jirgin yaki a Najeriya Damilola Adegboye ta bukaci a yi bincike kan musababbin mutuwar kanwartata, Tolulope Arotile. Damilola Adegboye, yayar marigayiya hafsan sojin sama Tolulope ta nuna shakku kan dalilin da aka bayar na rasuwar kanwarta, domin a cewarta, “ta yaya za a yi motar da ke juyowa […]
‘Yar uwar mace ta farko mai tuka jirgin yaki a Najeriya Damilola Adegboye ta bukaci a yi bincike kan musababbin mutuwar kanwartata, Tolulope Arotile.
Damilola Adegboye, yayar marigayiya hafsan sojin sama Tolulope ta nuna shakku kan dalilin da aka bayar na rasuwar kanwarta, domin a cewarta, “ta yaya za a yi motar da ke juyowa da baya za ta iya kashe ‘yar uwarta”.
Ta ce “Mu ‘yan uwanta ba mu gamsu da dalilin da aka bayar na rasuwarta ba, rundunar soji kwararu ne wajen gudanar da bincike, saboda haka muna bukatar su yi binciken da zai gamsar da mu.
“A ranar mutuwarta ina tare da ita a dakin da take a kwance, wani ne ya kira ta a waya cewa ta dawo bakin aiki, ina kyautata zaton babban hafsan sojin sama ne, ba ta ji dadin kiran ba domin sai da ta yi kamar ba za ta amsa kiran ba, amma na ce mata zan kai ta a mota.
“Bayan sa’a guda da kiran ta da aka yi sai ga labari na gani ta yanar gizo cewa ta gamu da mummunan lamari ta mutu, taya zan yarda, yarinyar da ni na sauke ta a mota cikin sa’a guda”, inji ta.
Za a tuna da marigayiya Tolulope
A bangare guda kuma Majalsiar Dokokin Jihar Kogi inda Tolulope ta fito ta amince da kudurin dokar sanyan suna marigayiya Tolulope domin tunawa da ita saboda gagarumar gudunmuwarta wajen yakar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Najeriya.
Bayan amincewa da kudurin dokar wanda dan majalisa Kilani Olumo mai wakiltar mazabar Tolulope ta Ijumu ya gabatar, Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar ta da gaggauta sanya sunan marigayiyar.
Abin da ya bambanta Tolulope
Tolulope ita ce hafsan sojin saman Najeriya ta farko mai tuka jirgin sama, kuma tana sahun farko a yaki da matsalar tsaro musamman a yankin Arewa ta tsakiya da Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ita ce aka fara yayewa kai tsaye a matayin hafsan sojin sama, bayan Grace Garba wadda ta fara aikin tun daga matsayin kurtu har ta zama hafsa.
Babban burin Tolulope tun tana ‘yar karama shi ne tuka jirgin yaki kuma shi ne abin da ta mayar da hankali a kai a lokacin da take kwalejin soja.
Mahaifanta sun bayyana ta a matsayin mai tsananin kaifin basira da kuma kwazo.
Ta fara tuka jirgin yaki a shekarar 2017 bayan kammala karatu a kwalejin kananan hafsohin soja ta Najeriya (NDA) da ke kaduna, inda ta samu digiri a fannin Kimiyyar Lissafi.
Ta yi karatun firamare da sakandarenta a makarantar ‘ya’yan sojojin sama ta Najeriya da ke Kaduna.
Rasuwarta
Tolulope ta rasu sakamakon raunukan da ta samu a kanta a hatsarin mota da ya ritsa da ita a barikin sojojin sama da ke Kaduna.
Yayin sanar da rasuwarta, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana kaduwa tare da kwatanta mutuwar a matsayin babban rashi
Rundunar ta yaba irin kwazon da Tolulope ta yi wajen yakar ‘yan fashin da sauran ‘yan bindiga a jihar Neja da yankin Arewa masu Yamma.
‘Yan Najeriya daga ko’ina sun yi ta juyayin rasuwarta tare da kwatanta ta a matsayin jaruma.