Toni Kroos zai yi ritaya daga kwallon kafa
Kroos zai buga wasansa na karshe a Gasar Zakarun Turai, wanda za a yi tsakanin Real Madrid da Dortmund, sannan ya wakilci kasarsa Jamus a Gasar Nahiyar Turai ta 2024
Fitaccen dan wasan Real Madrid da kasar Jamus, Toni Kroos, zai yi ritaya daga buga kwallon kafa.
Dan wasan zai buga wasan karshe na Gasar Zakarun Turai, wanda za a fafata tsakanin Real Madrid da kungiyar Dortmund.
Sannan zai wakilci kasarsa ta Jamus a Gasar Nahiyar Turai ta shekarar 2024 a matsayin gasannin karshe da zai taka leda.
Fitaccen dan jaridar kwallon kafa, Fabrizio Romano ne ya tabbatar da hakan, inda ya sanar da cewa, “A ranar 17 ga Yuli, 2014 ce aka gabatar da ni a matsayin sabon dan wasan Kungiyar Real Madrid, wanda ranar ce ta canja rayuwata a matsayin dan kwallo.
- ’Yan bindiga sun shiga hannu wurin ba wa sojoji cin hanci a Taraba
- Mahara sun kashe mutane 40 a Filato
“Bayan shekara 10, na yanke shawarar daga wannan kakar, zan dakata haka.Ba zan taba mantawa da nasarorin da na samu a nan ba.
“Ina godiya ga duk wanda ke da alaka da wannan kungiyar da taimakon da na samu har zuwa wannan mataki.
“Uwa-uba, ina godiya ga dimbin magoya bayan wannan kungiya, wadda ita ce ta daya a duniya bisa kaunar da suke nuna min daga farko da na zo, zuwa wannan lokaci.
“Ba wai Real Madrid kadai zan bari ba, kwallon kafar baki daya zan yi ritaya daga bugawa. Na dade ina da burin ganin na kammala buga kwallo ina cikin ganiyata.
“Yanzu babban burina shi ne Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai na 15. Hala Madrid,” in ji Kroos.