Tonon silili

  Tonon silili Wani magidanci ne suna zaune da matarsa suna hira, sai ta ce: “Bari in je in kawo maka abinci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa.” Sai ya ce: “Yauwa uwargida, kamar kin san kuwa yunwa nake ji.” Bayan ta kawo masa sai ya tambaye ta cewa: “Allah Ya sa dai wannan […]

Tonon silili
Tonon silili

 

Tonon silili

Wani magidanci ne suna zaune da matarsa suna hira, sai ta ce: “Bari in je in kawo maka abinci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa.” Sai ya ce: “Yauwa uwargida, kamar kin san kuwa yunwa nake ji.” Bayan ta kawo masa sai ya tambaye ta cewa: “Allah Ya sa dai wannan tumatur din miyar nan ba a gidan makwabcin nan namu kika sayo ba, kin san sai su sa mana guba a ciki.” Sai ta ce: kwarai, a nan na sayo, amma ka sha kurumin ka, kafi in ba ka abincin ma sai da na gwada ba karen gidan nan ya ci tukunna.” Maigida ya fara narkar abinci ba ji ba gani, suna haka sai ga ’yar aikin gidan ta shigo, ta ce: “Alhaji na manta ban fada maka ba cewa karen gidan nan ya mutu dazu.” Nan take Alhaji ya sare, ya ce: “Uwargida kafin in mutu ina so in nemi gafarar ki, mun haifi ’ya’ya biyu da ’yar aikin gidan nan.” Sai uwargidan ta ce: “Ni ma ka yafe mini, domin daga cikin ’yayanka 4, biyu ne naka, 2 na maigadin gidan nan ne.” Ana cikin haka sai maigadin ya yi sallama ya ce: “Alhaji wani ya zo ce mini in ba ka hakuri, shi ne ya doke karenka dazu da mota har ya mutu.”

Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382

Santin gyada

Wani Bafulatani ne ya je kiwo, ruwan sama ya yi masa duka, ya dawo gida yana ta kyarmar sanyi kamar zai mutu. Ganin haka ya sa matarsa ta hura masa wuta a cikin daki, sannan ta kawo masa gyada yana ci yana jin dumin wuta. Can da ya ji dadi sosai sai ya ce: “Kai, mu kan ko a lahira da ni da baffa da goggo wuta da gyada muka zaba.”

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja, 08100229688

Saurayin sauro

Wani sauro ne ya fara koya wa dansa tashi, har ya fara kwarewa. Ranar nan sai uban ya ce masa: “Ya kamata yau ka tashi kai kadai, domin in ga kwarewarka.” dan saurayin sauron nan ya bude fiffikensa ya tashi sama, ya yi shawagi. Bayan ya dawo, ya sauka sai uban ya tambaye shi cewa: “Shin ya ka ji lokacin da ka tashi?” Cikin farin ciki saurayin sauron ya gaya wa babansa cewa: “Wato abin da ya fi burge ni, shi ne irin yadda na ga duk inda na wuce mutane na yi mani tafi.” Uban ya kalle shi ya yi murmushi ya ce: “Yaro, ai ba tafi suke maka ba, kashe ka suke so su yi.”

Daga Mudassir Maishayi, 09025297045