Tonto Dikeh da Yul Edochie sun zama taurarin jaridar banguard na bana

A makon da ya gabata ne makaranta jaridar banguard suka zabi mawaki Tonto Dikeh da ’yar fim din Kudancin Najeriya, Yul Edochie a matsayin fitattun taurarin 2013 a fagen nishadantarwa.Shi dai Tonto, wanda ya shahara da wakarsa ta ‘Itz Oba’ ya samu nasara ne bayan ya doke Ebube Nwagbo da Colette Orji a yawan kuri’u. […]

Tonto Dikeh da Yul Edochie sun zama taurarin jaridar banguard na bana

Tonto Dike da Yul EdochieA makon da ya gabata ne makaranta jaridar banguard suka zabi mawaki Tonto Dikeh da ’yar fim din Kudancin Najeriya, Yul Edochie a matsayin fitattun taurarin 2013 a fagen nishadantarwa.
Shi dai Tonto, wanda ya shahara da wakarsa ta ‘Itz Oba’ ya samu nasara ne bayan ya doke Ebube Nwagbo da Colette Orji a yawan kuri’u. Ita kuwa Yul ta samu tata nasarar ce a yayin da ta doke Benson Okonkwo da Uti Nwachukwu.
Shi dai wannan tsarin gasa na zaben fitattun taurari a fagen nishadantarwa, inda ake neman mutane su kada kuri’a, kamfanin jaridar banguard ne ya fara shi a 2008, inda a wannan shekarar, Genebiebe Nnaji da Jim Iyke ne suka fara lashe shi, a yayin da Ini Edo ta zama ta biyu, yayin da Mercy Johnson ta samu matsayi na uku.
A 2009 ne kuwa, Omotola Jalade-Ekeinde da Desmond Elliot suka samu nasara. Inda Omotola ta doke Genebiebe Nnaji da Chika Ike, a yayin da shi kuma Elliot ya doke Chidi Mokeme da Richard Mofe-Damijo.