Tony Anenih ya rasu
Tsohon shugaban kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan ayyuka da gidaje Chief Tony Anenih ya rasu a jiya Lahadi. Mista Anenih, ya rasu yana da kimanin shekara 85 a duniya a wani asibiti da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya bayan ya sha fama da jinya. Daya daga cikin dan marigayin Anthony Anenih […]
Tsohon shugaban kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan ayyuka da gidaje Chief Tony Anenih ya rasu a jiya Lahadi.
Mista Anenih, ya rasu yana da kimanin shekara 85 a duniya a wani asibiti da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya bayan ya sha fama da jinya.
Daya daga cikin dan marigayin Anthony Anenih Junior ya tabbatar da rasuwa Mista Anenih.
Nan gaba kadan za’a sanar da ranar birnin Anenih.