Kananan Labarai

Kananan Labarai

Gobara ta lalata dukiya ta miliyoyin Naira a Damaturu

Wata gobarar da ake kyautata zaton ta samo asali ne daga wutar lantarki ta lalata dukiya ta milyoyin Naira a garin Damaturu fadar Jihar Yobe.

Gwamnatin Zamfara za ta inganta noman rani a bana

Gwamnatin Jihar Zamfara da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya za su inganta noman rani m usamman noman alkama sabod albarkar kasar noma da jihar ke da ita

Za a raba tan din hatsi 900 ga wadanda ambaliya ta shafa a Gombe

Minista a Ma’aikatar Gona ta Tarayya Alhaji Bukar Tijjani, ya ce za a raba tan din hatsi 900 ga wadanda ambaliya ta shafa.

Hadarin mota ya ci ’yan uwan Mataimakin Gwamnan Sakkwato takwas

Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Mukhtari Shagari ya rasa ’yan uwansa takwas a wani hadarin mota a ranar Litinin da ta gabata a Kwanar Kalgo

kanen Jonathan ya mutu a Abuja

Shugaba Goodluck Jonathan ya rasa kanensa mai suna Cif Meni Innocent Jonathan, wanda ya mutu a ranar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.