Labarai

Labarai

Bata-gari sun yi yunkurin wawushe kaya a Kasuwar Dawanau

An girke jami’an tsaro kimanin 800 bayan bata-gari sun nemi kutsawa su sace kayayyakin abinci a Kasuwar Dawanau da ke Kano da sunan zanga-zangar

Ina Jinjina Ga Masu Zanga-zanga —Gwamna Makinde

Gwamna Oyo ya nuna matukar farin ciki a kan yadda matasa suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa cikin lumana a jihar.

Saurayin Mai Awara Ya Watsa Mata Tafasasshen Mai A Zariya

Ya yi mata wanka da tafasasshen mai ne saboda ta yi masa magana bayan ya yi ta daukar awaran da take suya yana ta ci

Makiyaya Sun Yanke Hannuwan Manomi A Gonarsa A Borno

Wasu da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne sun sare hannuwan wani manomi bayan sun shiga gonarsa da dabbobinsu a Jihar Borno.

Jama’a sun dawo da kayan da aka sace a zanga-zangar yunwa a Gombe

Al’ummar Bolari sun dawo da kayayyakin da bata-gari suka sace a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa