Tornadoes ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta bana

kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes ta fara tace ‘yan wasan da za su fafata da sauran takwarorinsu a gasar kwallon kafar da za a yi a rukunin kwararru wanda za a fara kwanan nan.Jami’in Yada Labarai na kungiyar Mista George Daniya ne ya shaida wa wakilinmu cewa tuni Shugaban Majalisar Gudanar da kungiyar Malam […]

Tornadoes ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta bana
Tornadoes ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta bana

kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes ta fara tace ‘yan wasan da za su fafata da sauran takwarorinsu a gasar kwallon kafar da za a yi a rukunin kwararru wanda za a fara kwanan nan.
Jami’in Yada Labarai na kungiyar Mista George Daniya ne ya shaida wa wakilinmu cewa tuni Shugaban Majalisar Gudanar da kungiyar Malam Adamu Aliyu Muhammad ya amince wa kulob din tafiya Ilorin don samun horo kuma a kokarin tantance ’yan kwallon da za su haye kakar wasa mai zuwa
 kungiyar ta yada sansani a birnin Ilorin domin gudanar da tantancewa ta karshe da zai sa a zakulo zaratan ’yan wasan da za su murza leda a kakar wasa ta bana.  
Mista George Daniya ya ci gaba da cewa,”wannan wata dama ce muka samu da za mu zabi ’yan wasan da za su taiamaka mana a wasannin da za mu kara da abokan karawarmu  duk da cewa mu muka lashe gasar Super Four. Za mu hada wadanda muke da su a hannu da wadanda suka nuna sha’awar yi mana wasa domin samun nasarar da muka sa a gaba.
Jami’in ya nuna cewa Shugaban Majalisar ya yaba da irin rawar da wadanda suka jagoranci kungiyar suka taka muhimmiyar rawar da ta kai su ga samun nasarar da suka dade suna muradi,musamman sake komawa rukunin kwararrun ‘yan wasa daga lokacin da aka mayar da kungiyar rukunin da ke kasa da haka.
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello wanda ya samar musu da duk kayan aiki da gudunmuwar da suke nema domin tabbatar da an fara komai yadda ya kamata kuma a lokacin da ya dace.  Wannan ne ya sa suka kuduri aniyar taka rawar da kowa zai yi alfahari da ’yan wasan da suka dauka domin fafata wa a gasar ta bana.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa