Toshe shafin Facebook: ’Yan Rasha sun koma amfani da VPN
Kasar dai ta zargi Facebook da zama shafin masu tsattsauran ra’ayi
Kusan mako daya bayan hukumomin Rasha sun toshe dandalin sada zumunta na Facebook a kasar, rahotanni na cewa ’yan kasar da dama sun koma amfani da manhajar VPN don shiga shafin ta barauniyar hanya.
Manhajar dai na bai wa masu amfani da ita damar tsare sirrin na’urar da suke amfani da ita wajen shiga kowane irin shafi, ta yadda hatta wadanda aka toshe a kasar za a iya shigarsu ta hanyar amfani da ita.
- Rikicin APC: Za mu yi irin ta PDP 6 Gargadin Buhari ga ’yan jam’iyya
- Saudiyya ta zartar wa mutum 81 hukuncin kisa
Wani dan kasar mai suna Nikolay, wanda yake zaune a Turai, ya ce abokansa da ke cikin kasar yanzu haka sun koma amfani da manhajar ta VPN domin sadarwa da sauran mutane, a daidai lokacin da ake harsashen kasar za ta kara matsa kaimi wajen fito da sabbin hanyoyin dakile amfani da shafukan.
“Ana ta ba mutane shawarar su gaggauta fara amfani da manhajar tun da wuri,” inji Nikolay.
“Ta hanyar maye gurbin lambobin na’urorinsu da wasu da ba a sani ba, wadanda za su kasance na wata kasar ta daban, hakan na nufin mazauna Rasha za su iya shiga shafukan da aka toshe a kasar,” inji Simon Migliano, shugaban sashen bincike a Top10VPN.
Babban burin kasar dai bai wuce tace labarai da bayanan da ’yan kasar za su ci karo da su daga ketare ba, musamman a kan tankiyarta da Ukraine.
Ko a cikin makon nan dai sai da shafin Twitter ya yi zafin nama wajen yi wa manufofin amfani da shi kwaskwarima saaboda ’yan Rashar, don gudun kada su ma a toshe su a can.
A ranar Juma’a ne dai hukumomin Rasha suka matsa kaimi wajen takaita tasirin amfani da shafukan sada zumunta na kasashen Yamma, inda suka toshe shafukan Meta na Mark Zuckerberg, mallakin shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp, bayan sun zarge su da zama masu tsattsauran ra’ayi.
Ana dai ci gaba da fargabar cewa nan da wani lokaci akwai yiwuwar shiga shafukan intanet da dama su gagara a kasar ta Rasha.