Toshon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi ya zama Bunun Yawuri

Mai martaba Sarkin Yawuri Dokta Zayyanu Abdullahi, ya nada tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Abubakar Umar Warra a matsayin Bunun Yawuri da kuma Aliyu Ahmed Adamu a matsayin dan Isan Yawuri a bikin da ya samu halartar fitattun mutane daga sassan kasar nan.Sabon Bunun Yawuri Alhaji Abubakar Umar Warra an haife shi ne a […]

Toshon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi ya zama Bunun Yawuri
Toshon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi ya zama Bunun Yawuri

Mai martaba Sarkin Yawuri Dokta Zayyanu Abdullahi, ya nada tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Abubakar Umar Warra a matsayin Bunun Yawuri da kuma Aliyu Ahmed Adamu a matsayin dan Isan Yawuri a bikin da ya samu halartar fitattun mutane daga sassan kasar nan.
Sabon Bunun Yawuri Alhaji Abubakar Umar Warra an haife shi ne a garin Warra da ke karamar Hukamar Ngaske a 1942, inda ya fara neman ilimi da karatun allo, daga bisani ya shiga makarantar firamare ta garin Warra a 1957, sai sakandaren Birnin Kebbi da Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Alhaji Abubakar Warra ya yi aiki a wurare da dama tare da rike mukamai daban-daban da suka hada da Odita Janar a tsohuwar Jihar Sakkwato da Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi da kuma Kwamishinan Zabe na kasa.
Shi kuwa sabon dan Isan Yawuri Alhaji Aliyu Ahmed Adamu an haifi shi ne a 1966 a garin Gungun Sarki da ke karamar Hukumar Yawuri, kuma ya halarci makarantar firamare ta Gungun Sarki da sakandaren Yawuri da kuma Jami’ar Tafawa balewa da ke Bauchi. Alhaji Aliyu A. Adamu fitaccen dan jarida ne da ya fara aiki da jaridar National Concord a 1988.
A jawabinsa, jim kadan bayan kammala nadin, Sarki Zayyanu Abdullahi ya ce, ya nada mutanen biyu ne, saboda lura da irin dimbin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban masarautar da yadda suke taimakwa wa duk wani al’amari da ya shafi al’ummarsu.
Sarkin ya ce yana fata za su ci gaba da nuna kishi da tallafawar da sukeyi ga al’ummar domin ci gaban masarautar Yawuri da Jihar Kebbi da Najeriya baki daya.
A jawabin godiya Alhaji Abubakar Umar Wara, ya gode wa Mai martaba Sarkin Yawuri da ’yan majalisarsa kan goyon bayan da suka ba shi har Allah Ya tabbatar masa da wannan sarauta.
Ya tabbatar wa Sarkin cewa da yardar Allah shi da dan Isan ba za su ba Sarkin da ’yan majalisarsa kunya ba.