Tosin Oke ya ciwo wa Najeriya lambar zinare a wasan tsalle

dan wasan tsalle na Najeriya, Tosin Oke ya kara yawan lambobin zinaren da Najeriya ta ci a gasar wasanni ta Afirka da za a kammala gobe a kasar Kongo Brazzabille, bayan da ya zamo zakara a gasar Tsallen Maza a ranar Litinin da ta gabata. Kafin wannan nasara Oke ya yi barazanar kaurace wa gasar, […]

Tosin Oke ya ciwo wa Najeriya lambar zinare a wasan tsalle
Tosin Oke ya ciwo wa Najeriya lambar zinare a wasan tsalle

dan wasan tsalle na Najeriya, Tosin Oke ya kara yawan lambobin zinaren da Najeriya ta ci a gasar wasanni ta Afirka da za a kammala gobe a kasar Kongo Brazzabille, bayan da ya zamo zakara a gasar Tsallen Maza a ranar Litinin da ta gabata. Kafin wannan nasara Oke ya yi barazanar kaurace wa gasar, amma daga baya ya amince ya halarta don kare kambin da yake rike da shi shekara hudu da suka gabata a gasar da aka gudanara a Maputo.
dan wasan da ke zaune a Landan ya yi tsalle mai tsawon mita 17, inda ya lashe lambar zinare, kuma ya kara kafa bajinta kan tsallensa na baya da ya yi na mita 16.65 da ya samu lambar zinare a Maputo. Ana sa rai Oke ya haskaka a gasar Olempik na Rio a badi, musamman ganin yana cikin mutum takwas da suka fi iya tsalle a gasar tsalle ta duniya da aka gudanar a Beijing.
Wani abin sha’awa shi ne dan wasan Najeriya, Olumide Olamigoke ne ya lashe lambar azurfa a gasar ta tsalle ajin maza.
Sai dai a bangaren mata, ’yar Najeriya Doreen Amata ta kasa kare kambinta na gwarzuwar Afirka inda ta zo ta biyu da lambar azurfa a bayan Lissa Labiche wadda ta lashe azurfa bayan ta yi tsallen mita 1.95. A sauran wasannin da aka kammala a ranar Litinin Tyron Akins ya zo na uku ne a gudun tsallen shinge na mita 110, yayin da wakilan jefar nauyi na mata da ke wakiltar Najeriya suka kare ba tare da samun kowace lamba ba.