Tottenham ta dauki Conte a matsayin sabon Kocinta

Kungiyar ta dauke shi ne bayan ta Kori Nuno Espirito Santo.

Tottenham ta dauki Conte a matsayin sabon Kocinta

Antonio Conte

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauko Antonio Conte bayan ta sallami tsohon kocinta Nuno Espirito Santo wanda ya yi wata hudu kacal a kungiyar.

Conte, wanda tsohon kocin kungiyar Chelsea ne, ya bayyana farin cikinsa na dawo wa harkar ta kwallon kafa bayan barin kungiyar Inter Milan, inda ya lashe kofin Seria A a kakar bara.

A cewarsa, “Ina matukar farin ciki da dawowa horar da ’yan wasa, musamman ma a Gasar Firimiyar Ingila.

“Kungiyar Tottenham Hotspur kungiya ce babba wadda take da daya daga cikin manyan filin wasa na a zo a gani.

“A kakar bara aka so a daura wannan aure, amma bai yiwu ba, kasancewar lokacin ban jima da rabuwa da Inter Milan ba. Yanzu a shirye nake domin ciyar da kungiyar nan gaba.”

A lokacin da yake Chelsea, Conte ya lashe kofi biyu: Firimiyar Ingila da Kofin Kalubale na Ingila.

Ya sanya hannu a kwantiragin ne na tsawon wata 18.