Tottenham ta yi sukuwar sallah a kan Manchester United
Manchester United na mataki na 12 a gasar Firimiyar Ingila ta bana.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta yi fata-fata da Manchester United har gida da ci 3 da nema.
Al’amura na ci gaba da dagulewa Manchester United, yayin da ta ke a mataki ka 12 a Gasar Firimiyar Ingila.
- “Sojoji sun kasa kawo ƙarshen Turji kamar yadda Jonathan ya yi wa Boko Haram”
- Ana musayar yawu tsakanin Gwamna Lawan Dare da Matawalle
Manchester United da Tottenham sun kara ne da yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Old Trafford.
Tottenham ta fara jefa ƙwall9 ne ta hannun ɗan wasanta, Johnson a minti na uku da fara wasa.
A minti na 33 ɗan wasa Kulusevki ya sake jefa wa Tottenham ƙwallo ta biyu a raga.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Dominic Solanke ya jefa ƙwallo ta uku a minti na 77.
A gefe ɗaya kuma alƙalin wasa ya bai wa ɗan wasan tsakiyar Man United, Bruno Fernandez jan kati, wanda hakan ya sa ƙungiyar ƙare wasan da mutum 10 a fili.
Kobi Mainoo da Mason Mount sun samu rauni a wasan.