Tozarta hanyar tsige shugabanni
Saura ’yan makonni a kawo karshen wa’adin gwamnatoci masu ci, guguwa da barazanar tsige-tsige na ta kadawa a wasu jihohin kasar nan. A Jihar Adamawa, wakilan Majalisar Dokokin Jihar tara sun yunkura bayan da suka dawo daga hutun mako uku a watan Afrilu, inda suka zauna a Gidan Gwamnati da ke Yola suka bayyana cewa […]
Saura ’yan makonni a kawo karshen wa’adin gwamnatoci masu ci, guguwa da barazanar tsige-tsige na ta kadawa a wasu jihohin kasar nan.
A Jihar Adamawa, wakilan Majalisar Dokokin Jihar tara sun yunkura bayan da suka dawo daga hutun mako uku a watan Afrilu, inda suka zauna a Gidan Gwamnati da ke Yola suka bayyana cewa sun tsige Shugaban Majalaisar Ahmadu Umaru Fintiri.
Fintiri wanda kasa da wata daya wa’adin majalisarsa zai kare ya ki amincewa da yunkurin, inda ya ayyana wakilan majalisar da suka yi wancan yunkuri da korarru.
Sai kuma ga wakilai 12 na Majalisar Dokokin Jihar Kebbi suka bi sahu, inda suka bayyana cire shugabansu, Hassan Shalla da mataimakinsa Ja’afar Mohammed, a wani abu da suka ce zaman gaggawa da daya daga cikinsu, Abubakar Sabo ya jagoranta, kuma sun zabi Aminu Musa Habib Jega a matsayin shugaban majalisar. Ba su tsaya a nan ba, washegari ’yan majalisar suka aika wa Gwamnan Jihar Sa’idu Usman dakingari takardar sanarwar za su tsige shi.
Kuma a daidai wannan lokaci ne wakilai 18 daga cikin 27 suka tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Adamu Usman, kuma Isa Kawu na Mazabar Bidda ta daya ya maye gurbinsa. Kamar yadda ya faru a Kebbi, ’yan majalisar sun yi yunkurin tsige Gwamnan Jihar Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, wanda ya yi gaggawar taka musu birki.
Domin kada guguwar tsige-tsigen ta bar su a baya, wakilan Majalaisar Dokokin Jihar Enugu ma sun fara yunkurin tsige Gwamna Sulliban Chime bisa zargin almundahana da rashin bin ka’ida. ’Yan majalisa 14 a karkashin jagorancin shugaban majalisar Eugene Odo suka zauna suka umarci Akawun Majalisar ya aika takardar sanarwar tsigewa ga Chime saboda bai samu amincewar majalisar nay a ciyo bashin Naira biliyan 11 alhal saura kasa da mako uku ya bar kujerarsa.
Makonni kadan kafin faruwar wadannan abubuwa, an cire Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo, Ali Olanusi ta hanyar tsigewa daga bangaren majalisar jihar, yayin da a makwabciyar jihar ta Ekiti Gwamna Ayo Fayose da mataimakinsa ke kokarin kwatar kansu daga mafi rinjayen ’yan majalisarsa da suka aike musu da sanarwar tsigewa.
Abin da yake fili a dukkan wadannan abubuwa musamman duk da kurar da dauki-dorar da ake zargin gwamnoni da yi a zabubbukan da suka gabata, dalilan yunkurin ba su da alaka da bin tanade-tanaden tsarin mulki illa ramuwar gayyar siyasa.
Sai dai ya kamata a fahimci tsigewa ba karamar makami ne da za a rika wasa da shi ba, a tsakanin wadanda aka ba su wannan amana. Idan ba a sanya aya kan haka ba, za su mayar da ita kanta dimokuradiyyar abar dariya da zunde da wasu kyawawan dokokinta da suke kaimi wajen tabbatar da bin ka’ida kamar yadda tsarin mulkin Najeriya yaken nufi.
Koda akwai lokutan da ake ganin wani jami’in gwamnati ya yi ba daidai ba, ya kamata hanyar tsige shi ta zamo ita ce hanya ta karshe bayan an bi dukkan hanyoyin yi masa gyara ba a cimma nasara ba. Amma a yanayin da wani jami’i kamar Gwamnan jiha da mafi yawan jama’a suka zaba, a ce wasu ’yan kalilan da ba su fi cikin cokali ba, za su zauna su yanke hukuncin tsige domin bata masa harkokin siyasarsa na gaba sam bai dace ba. Abin da ke da muhimmanci ga tsige-tsigen ko abin da ke wajabta tsigewar, wajibi ne ya zamo ya dara abin da ake gani a yau, kuma duk wani dungu da za a yi game da dalilan da za su sa a tsige wani jami’i, bai kamata su zamo hanyoyin da wasu kalilan din ’yan majalisa za su tozarta ka’idojin da ake bi ba waje aiwatar da hakan, wajibi ne ’yan majalisar su kasance masu tunani da taka-tsantsan a duk lokacin da za su bi wannan hanya.