…Trump bai da hankali- Shugban Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa ya bayyana Shugaba Trump a matsayin mara hankali bisa yadda ya ayyana birnin na kudus a matsayin babban birnin Isra’ila. Trump dai da shugaban na Koriya ta Arewa sun dade suna sa zare tsakaninsu, inda suke yawan cacan baki, da caccakar juna da cin alwashin juna, musamman saboda shirin Koriya ta […]

…Trump bai da hankali- Shugban Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa ya bayyana Shugaba Trump a matsayin mara hankali bisa yadda ya ayyana birnin na kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Trump dai da shugaban na Koriya ta Arewa sun dade suna sa zare tsakaninsu, inda suke yawan cacan baki, da caccakar juna da cin alwashin juna, musamman saboda shirin Koriya ta Arewar na makamashin Nukiliya.

Yanzu shi ma shugaban na Koriya ta Arewa ya shiga cikin sahun wasu kasashen duniya da suka yi Allah wadai da shugaba Trump saboda yanke shawarar ayyana kudus a matsayin birnin Isra’ila., inda ya ce wannan ayyanawar “Zalunci ce da rashin hankali.”

“Kasancewar wannan mara hankalin yana so ya janyo rikici tsakanin kasashe na Majalisar dinkin Duniya, wannan ba a bin mamaki ba ne,” a cewar mai magana da yawun ma’aikatan harkokin wajen kasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na KCNA ya ruwaito.

“Wannan lamarin ya nuna wa duniya wanda ba ya san zaman lafiyan duniya baki daya.”

Kafar ta KCNA ta ruwaito, Koriya ta Arewa tana cewa ta yi Allah wadai da amincewa da birnin kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, sannan kuma ta nuna goyon baya ga Falasdinawa da sauran Larabawa da suke fafutukar kwato ‘yancinsu. Sannan kuma jawabin ya kara da cewa “kasar Amurka ce da alhakin duk wani matsala da hakan zai iya janyo wa.”