Trump da Hillary na ci gaba da samun nasara

A yayin da ake ci gaba da kidayar kuri’u a zaben fidda-gwani na ’yan takarar Shugaban kasar Amurka a karkashin jam’iyyun Republican da Democrats a kasar Amurka, wadanda aka gudanar a jihohi 11 da ake kira Babbar Talata (Super Tuesday,) manyan ’yan takara biyu Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrats suna ci […]

Trump da Hillary na ci gaba da samun nasara
Trump da Hillary na ci gaba da samun nasara

A yayin da ake ci gaba da kidayar kuri’u a zaben fidda-gwani na ’yan takarar Shugaban kasar Amurka a karkashin jam’iyyun Republican da Democrats a kasar Amurka, wadanda aka gudanar a jihohi 11 da ake kira Babbar Talata (Super Tuesday,) manyan ’yan takara biyu Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrats suna ci gaba da samun nasara.
Sakamakon farko na kuri’un da aka kidaya ya nuna cewa Donald Trump ya lashe jihohi bakwai, yayin da Miss Clinton ta lashe jihohi bakwai.
Jihohin Alabama da Georgia da Tennessee da birginia na daga cikin jihohin da ’yan takarar biyu suka lashe.
Mista Trump ya sha kaye a hannun Sanata Ted Cruz a jihohin Tedas da Okhahoma da Alaska inda ya hana Trump samun gagarumar nasara.
Mutumin da ke son yi wa Jam’iyyar Democrats takara, Bernie Sanders, ya samu nasara a jihohi hudu ciki har da Oklahoma da kuma jiharsa ta bermont.
Sanata Marco Rubio na Florida ya ci jiha ta farko a zaben da aka gudanar a Minnesota.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya