Trump ya ayyana birnin kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila
Shugaba Tump ya cika alkawarin da ya yi wa masu goyon bayan Israila a lokacin yakin neman zabe, amma a wannan karon ya tabo daya cikin batutuwa masu zafi a rikicin da ke tsakanin Israila da Palasdinu wato makomar birnin kudus kamar yadda BBC ta ruwaito. Shugaba Trump ya kira wasu shugabannin kasashen Larabawa ta […]

Shugaba Tump ya cika alkawarin da ya yi wa masu goyon bayan Israila a lokacin yakin neman zabe, amma a wannan karon ya tabo daya cikin batutuwa masu zafi a rikicin da ke tsakanin Israila da Palasdinu wato makomar birnin kudus kamar yadda BBC ta ruwaito.
Shugaba Trump ya kira wasu shugabannin kasashen Larabawa ta wayar tarho domin ya fada musu aniyarsa ta mayar da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tel Abib zuwa birnin kudus.
Da yake ayyana birnin a matsayin babban birnin kasar, Trump cewa ya yi “A yau mun amince da zahirin abin da ke kasa na cewa Birnin kudus ne babban birnin kasar Isra’ila,” inji Trump. Sannan ya kara da cewa amincewa da birnin a matsayin babban birni “Abu ne da ya dace.”
A nasa jawabin, jim kadan bayan ayyana birnin a matsayin babban birni, Firayi ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yaba wa shugaba Trump, inda ya ambaci wannan ayyanawar a matsayin abin tarihi, sannan ya ce ba za ta hana kowa gabatar da ibada ba a birnin. “Muna matukar godiya ga Shugaba Trump bisa jajircewarsa wajen daukan wannan matakin,” inji Netanyanhu.
Sai dai Sarki Salman na Saudiyya ya fada masa cewa duk wani yunkuri irin wannan zai harzuka musulmi a kasashen duniya.
Ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta yi gargadi a kan duk wani mataki da ka iya kawo nakasu a kokarin da ake wajen ganin an cimma maslaha tsakanin Israila da Palasdinu.
Amma tun farko mai magana da yawun fadar White House Sarah Sanders, ta ce Shugaba Trump ya ce zai ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin idan ya dauki wannan mataki.
Isra’ila dai ta dauki birnin kudus a matsayin babban birinin kasar, yayin da Falasdinu kuma suka ayyana gabashin kudus a matsayin wurin da zai kasance babban birninsu idan sun kafa tasu kasar.
kasar Amurka ta zama kasa ta farko da ta ayyana birnin kudus a matsayin babban birni tun kafuwar Isra’ilar a shekarar 1948.