Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka
Gwamnatin Trump ta kare matakin, inda ta ce hakan zai kare iyakokin ƙasar.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin kama ’yan gudun hijira marasa takardun izinin zama a makarantu, coci-coci, da asibitoci a faɗin ƙasar.
Ma’aikatar Tsaron Ƙasa ta Amurka (DHS), ta bayyana cewa waɗannan wuraren ba za a sake ɗaukar su a matsayin wuraren kariya daga bincike ba.
- ‘Nan da shekaru 2 za a nemi likitoci a rasa a Nijeriya’
- ’Yan fashi sun hallaka mutum 7 a harin Kasuwar Ngalda da ke Yobe
Wannan mataki ya bai wa Hukumar Shige da Fice ta Amurka (ICE) damar gudanar da kamen mutane a waɗannan wuraren.
Sabon umarnin ya kawo ƙarshen dokokin da suka shafe sama da shekaru 10 suna kare irin waɗannan wuraren.
Har ila yau, an dawo da dokar korar gaggawa, wadda ke bai wa ICE damar korar duk wanda ba zai iya nuna cewa ya yi zama na tsawon shekaru biyu a Amurka ba.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama da shugabannin addini sun soki wannan mataki.
Sun ce matakin zai hana ’yan gudun hijira samun kulawa, ilimi, da taimakon gaggawa, tare da haifar da tsoro a zukatan jama’a.
Sai dai, gwamnatin Trump ta kare matakin, inda ta ce hakan wani muhimmin ɓangare ne na tsaron iyakokin ƙasar.