Trump ya ce zai bar Sadik Khan ya je Amurka
Attajirin nan da ake sa ran zai tsawaya jam’iyyar Republican takarar shugabancin Amurka, Donald Trump, ya ce zai bar sabon Magajin birnin Landan, Sadik Khan, ya ziyarci kasar idan ya lashe zabe.Trump dai ya yi kaurin suna wajen kin jinin Musulmi, inda ya ce zai hana su shiga kasar, idan ya ci zaben shugabancin Amurka.Sai […]
Attajirin nan da ake sa ran zai tsawaya jam’iyyar Republican takarar shugabancin Amurka, Donald Trump, ya ce zai bar sabon Magajin birnin Landan, Sadik Khan, ya ziyarci kasar idan ya lashe zabe.
Trump dai ya yi kaurin suna wajen kin jinin Musulmi, inda ya ce zai hana su shiga kasar, idan ya ci zaben shugabancin Amurka.
Sai dai a wata hira da ya yi ya ce “Akwai mutanen da dokar [hana Musulmi zuwa Amurka] ba za ta shafa ba”, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Mista Trump ya ce ya yi matukar farin ciki da Sadik Khan ya zama Magajin Birnin Landan.
Sadik Khan ya taba cewa ba zai kai ziyara Amurka ba, idan Trump ya ci zabe sakamakon haramcin da ya yi wa Musulmi na shiga kasar.
A ranar Asabar ne, Musulmi na farko da ya kasance Magajin Garin Landan karkashin babbar jam’iyar adawar Birtaniya ta Labour, Sadik Khan ya sha rantsuwar fara aiki, bayan ya lashe zaben da aka gudanar a makon jiya da gagarumin rinjaye.
Mista Khan dai, dan wani direban bas dan cirani daga kasar Pakistan, ya ce yana so ya wakilici ko wane bangare da al’ummar birnin. Ya ce burinsa shi ne ya tabbatar da cewa daukacin mazauna birnin Landan sun samu damar da ta kamata su samu.