Trump ya ce zai bar Sadik Khan ya je Amurka 1
Shugaban Amurka Barack Obama ya shirya kai ziyara garin Hiroshima da ke kasar Japan, wanda wannan shi ne karon farko da wani shugaban Amurka zai kai ziyara garin, wurin da Amurka ta jefa wa makamin kare dangi a watan Agustan shekarar 1945 lokacin Yakin Duniya na Biyu, inda ya kashe mutane akalla dubu 129.Tsawon shekaru […]
Shugaban Amurka Barack Obama ya shirya kai ziyara garin Hiroshima da ke kasar Japan, wanda wannan shi ne karon farko da wani shugaban Amurka zai kai ziyara garin, wurin da Amurka ta jefa wa makamin kare dangi a watan Agustan shekarar 1945 lokacin Yakin Duniya na Biyu, inda ya kashe mutane akalla dubu 129.
Tsawon shekaru 70 da suka gabata, kusan ko wane shugaban Amurka yana kauracewa ziyarar wadannan wuraren biyu da Amurka ta yi wa barna, wato garuruwan Hiroshima da Nagasaki.
Fadar White House ta ce Shugaba Obama zai ziyarci Hiroshima bisa rakiyar Firaministan Japan Shinzo Abe a ranar 21 zuwa 28 ga wannan watan, lokacin da zai kai ziyara a kasashen bietnam da kuma Japan.
Mataimakin Mai Bai wa Shugaba Obama Shawara kan Harkokin Tsaro, Ben Rhodes, ya ce ba ya tsammanin cewa shugaba Obama zai roki gafarar wannan harin bam din da aka kai Hiroshima da Nagasaki ba.
Ya ce “ko kusa Shugaba Obama ba zai sake duba wannan batun harin bam da aka a Hiroshima ba a karshen Yakin Duniya na Biyu, maimako zai duba gaba ne domin abin da zai ciyar da kasashen biyu gaba.”
Ziyarar ta zo dai-dai da lokacin da aka kwashe shekaru 75 bayan Tokyo ta kai harin ba-zata ga sojojin Amurka da ke gabar tekun Jihar Hawaii. Kodayake, kasashen biyu sun zamo manyan kawayen juna bayan Yakin Duniya na Biyu.
Shugaba Obama zai tafi kasar ne da zummar ya gana da shugabannin kungiyar kasashen nan Bakwai da Suka Fi Kowa Arziki a Duniya. Kuma daya daga cikin dalilan ziyartarsa Hiroshima shi ne ya kara jadda da kudirinsa na ganin cewa gwamnatin Amurka ta ci gaba da ba da gudunmuwarta ga harkokin tsaro a duniya, domin ci gaba da samun kyakkyawar tsaro a kowane kusurwa ta duniya.
Ko cikin watan da ya gabata sai da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry, ya kai ziyara Hiroshiman, inda ya ce ziyararsa tamkar sharar fage ce ta jaddada wa duniya cewa Amurka tana nan, tana iyaka bakin kokarinta na ganin cewa duniya ta kaucewa barazanar makamin Nukiliya daga wasu kasashen duniya.