Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA

Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yaɗa shirye-shiyenta cikin harsuna 40.

Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA.

Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna.

Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke ƙarƙashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba.

Haka kuma tuni Trump ɗin ya soma ɗaukar wasu matakai waɗanda suka haɗa da soke kwantiragin da VOA ɗin ke da shi na amfani da labaran kafafen watsa labarai masu zaman kansu daga ciki har da kamfanin dillancin labarai na Amurka wato AP.

Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani.

Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya.

Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin Amurka kan me hakan ke nufi, sannan babu wanda zai iya fahimtar ko an rufe kafofin baki ɗaya ke nan.

Shugaban ƙungiyar ’yan jarida a Amurka, William McCarren ya ce wannan ba abin alheri ba ne ga duniya da kuma aikin jarida baki ɗaya, musamman a wannan zamani da ake yaƙi da labaran bogi.

Tuni dai Shugaba Trump ya naɗa ’yar jarida Kari Lake a matsayin daraktar hukumar da za ta kula da rushe waɗannan hukumomi, waɗanda ya zarga da yaɗa labaran nuna masa ƙiyayya.

Sama da shekaru 80 ke nan da kafa VOA wadda ke yaɗa shirye-shiyenta cikin harsuna 40, ta rediyo da talabijin da intanet da shafukan zumunta na zamani.