Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa
Trump ya dakatar da aiwatar da dokar da ta hana amfani da TikTok a Amurka har na tsawon kwanaki 75.
Sabon shugaban ƙasa Donald Trump, ya janye Amurka daga ƙasashen da ke tallafa wa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Wannan na zuwa ne yayin da Trump ya rattaba hannu kan wasu gomman dokokin zartawa na ikon shugaban ƙasa, inda ya ɗauki matakan da suka shafi shige da fice, sauyin yanayi, haƙƙin Ƙasa, da sauran batutuwan da suka jawo hankalin duniya.
- Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa
- Ba mu ba sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Katsina
Donald Trump ya sanya hannu kan dokokin ne jim ƙadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar Amurka na 47 a ranar Litinin.
Wasu daga cikin umarnin da ya sanya hannu sun cika alƙawarin da ya yi wa magoya bayansa a zaɓen 2024, yayin da wasu matakan, kamar ficewar Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ba a yi tsammani ba.
Da yake kare matakin janye ƙasar daga hukumar lafiya ta duniya, Mista Trump ya ce Amurka ke ba da kaso 20 cikin ɗari na ƙudin gudanarwarta, amma ta gaza taɓuka abin a zo a gani, musamman bayan ɓarkewar annobar Coronavirus.
Karo na biyu ke nan da Trump ke fitar da Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma yarjejeniyar sauyin yanayi ta birinin Paris da aka cimma a shekarar 2015 domin rage gurɓatacciyar iska, kafin Joe Biden ya sake mayar da ƙasar cikinta.
Trump ya soke wasu umarnin tsohon Shugaba Joe Biden da suka tallafa wa shirye-shiryen daidaito da haɗin kai, musamman waɗanda suka shafi haƙƙin ’yan luwaɗi da maɗigo (LGBTQ), yana bayyana cewa daga yanzu, gwamnatin Amurka za ta riƙa amfani da jinsi biyu ne kawai — namiji da mace.
Trump ya kuma dakatar da aiwatar da wata doka da ta haramta amfani da TikTok a Amurka har na tsawon kwanaki 75, inda ya ce dole ne babban kamfanin mamallakin TikTok ByteDance ya sayar da kaso 50% na hannun jarinsa ga Amurka.
Trump ya soke takunkumi da aka sanya kan wasu masu zaune a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka zarga da cin zarafin Falasɗinawa, matakin da ya rushe dokar da gwamnatin Biden ta kafa.