Trump ya kaddamar da makon kayayyakin da aka hada a Amurka

A ranara Litinin da ta gabata ne shugaban kasar Amurka donald Trump ya kaddamar da makon kayayyakin da aka hada a kasar Amurka a birnin Washington.  bikin wanda aka shirya domin murnar kasuwanci da kere kere na kasar Amurka tare da nuna abubuwan da ake kerawa a jihohi 50 na kasar. Amma sai dai duk […]

Trump ya kaddamar da makon kayayyakin da aka hada a Amurka

A ranara Litinin da ta gabata ne shugaban kasar Amurka donald Trump ya kaddamar da makon kayayyakin da aka hada a kasar Amurka a birnin Washington. 

bikin wanda aka shirya domin murnar kasuwanci da kere kere na kasar Amurka tare da nuna abubuwan da ake kerawa a jihohi 50 na kasar.

Amma sai dai duk da cewa bikin ya yi armashi matuka, an sa wa bikin alamar tambaya ganin cewa kasuwancin shugaban kasar da iyalansa da kamfanonin kasashen ketare yake yi.

Yahoo ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na gidan gwamnatin Amurka Sean Spicer ya bayana a ranar bikin cewa yana daya daga cikin alkawarin da shugaba Trump ya yi a alokacin fafutukar neman zabe domin “Taimakawa ma’aikatan Amurka”, sannan kuma Spicer ya kara da ambaton karfin ikon Trump na “Yin amfani da ababen da aka hada a kasar Amurka, sannan kuma ya nuna cewa wannan shirin ba karamin abun tarihi ba ne ga kasar.

Sai dai kuma a wani bangaren, wasu sun kushe shirin domin a cewar su, shirin ba mai daurewa ba ne

Kafar yada labarai ta Yahoo ta tambaya Spicer ko shirin amfani da kayayyakinn da aka hada a Amurka zai hada da kamfanonin Trump.

Kamfanonin Trump, wadanda suke hada kayayyaki daban dabam masu dauke da tambarin “Trump” suna da dadadden tarihin yin aiki daga kasashen ketare. A shekarar da ta gabata, jaridar Washington Post ta yi wani bincike inda ta gano cewa ababen da kamfanin Trump ke hadawa a kasashen waje sun hada da riguna, gilasai, kayan gida da sauransu.

A ranar bikin “Kayayyakin da aka hada a Amurka”, dan jarida Sam Stein na daily beast ya ziyarci shagon kayan bayar da kyaututtukan Trump inda ya samu kayayyaki daga kasashen Chana, bietnam da Peru. Sannan kuma diyar Trump, Ibanka wadda ita ma mai’aikaciya ce a gidan gwamnatin tana amfani ne da kayayyakin da aka hada a kasashen waje.

Spicer ya bayar da amsar da aka tambayeshi a kan yanayin kasuwancin shugaba Trump a kasashen waje da cewa manufar shugaba Trump ita ce tabbatar da cewa “dukkan kamfanoni za su iya daukan ma’aikata a kasar, su fadada ayyukan su a kasar, sannan su hada ababen da suke hadawa a kasar.” Sannan ya kara da cewa “bai kamata ba” ya yi bayani a kan kasuwancin shugaba Trump a matsayin shi na ma’aikacin gidan gwamnati. Amma sai dai kuma ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa da suke sa wa kamfanoni suke samun saukin aiki a kasashen ketare.

“A game da kamfanonin shugaba Trump, bai kamata in yi bayani ba a kan abin da ya shafe kamfanonin. Amma ina tabbatar muku da cewa akwai wasu abubuwa da kamfanonin ke bukata da ba a samu a wannan kasar,” inji Spicer.

Sannan kuma Spicer ya ce shugaban Trump na kokari wajen canja tsarin.

“ba zan yi magana  a kan wani kaya ba ko kamfani, amma dai manufar ita ce a fadada harkar kasuwanci da zuba jari a kasar nan, sannan kuma a tallafa wa ma’aikatan Amurka. Wannan ita ce babbar manufar,” inji Spicer.

 bayan kammala jawabin, kafar Yahoo ta sake tambayar Spicer a kan ko shugaba Trump zai nuna shugabanci ta hanyar nuna misali da shi kan shi ta hanyar dawo da ayyukan kamfanoninshi  gida, inda nan take Spicer ya kara nanata cewa “bai kamata” ba ya yi magana a kan kasuwancin gidan shugaban.

“bai kamata ba na yi magana a kan kasuwancin gidan shugaban kasa. Amma zan sake tabbatar muku da manufar shugaban kasar na fadada harkar kasuwanci a kasar nan, da kuma dawo da kamfanoni kasar,” inji Spicer.

Spicer ya kara da cewa a matsayin Trump na tsohon dan kasuwa, ya san asalin abubuwan da ke sa wa kamfanoni suna ficewa daga kasar Amurka.

“A matsayin shugaba Trump na tsohon dan kasuwa, ya san asalin abubuwa da suke kawo cikas ga ci gaban kasuwanci a kasar nan, musamman kudin haraji ga wadanda suke so su fadada kasuwancinsu a kasar kuma suke bukatar wasu muhimman abubuwa da ba za su samu ba saboda yanayin tsarin kudin haraji, da kuma dokokin kasuwancin kasar,” inji Spicer.