Trump ya kusa zama dan takarar Republican
Donald Trump ya zama mutumin da zai yi wa jam’iyar Republican takarar shugabancin Amurka bayan kayen da ya yi wa abokin takararsa Ted Cruz a zaben fitar da gwani na Jihar Indiana ya tilasta masa janyewa daga yin takarar.Yanzu dai Mr Trump, wanda ba shi da farin jini a wajen ‘yan jam’iyyar, ya share hanyar […]
Donald Trump ya zama mutumin da zai yi wa jam’iyar Republican takarar shugabancin Amurka bayan kayen da ya yi wa abokin takararsa Ted Cruz a zaben fitar da gwani na Jihar Indiana ya tilasta masa janyewa daga yin takarar.
Yanzu dai Mr Trump, wanda ba shi da farin jini a wajen ‘yan jam’iyyar, ya share hanyar samun wakilai 1,237 da ake bukata domin tsayawa takarar shugabancin kasar.
Hakan dai wani abin mamaki ne, ganin cewa mutanen ba su dauke shi da muhimmanci ba a lokacin da ya fara yakin neman zabe a bara.
Har ila yau, Bernie Sanders ya doke Hillary Clinton a zaben fitar da gwani na jam’iyyar Democratic a Jihar ta Indiana.
Sai dai har yanzu ita ce ke gaba a yawan jihohin da suka lashe.
Ya ce Clinton tana tunanin an kammala yakin neman zabe, yana mai cewa hakan kuskure ne.
Hakazalika, a farkon makon nan ne Mista Trump, ya zafafa sukar manufofin huldar kasuwanci da China, yana zarginta da yi wa tattalin arzikin Amurka zagon kasa.