Kasashen Waje• Created December 7, 2017 12:23
Trump ya rura wutar rikici-Kungiyar Hamas
Kungiyar Hamas ta ce Shugaban Amurka Donald Trump ya kunna wutar rikici ne kawai tsakanin kasashen Larabawa bayan day a sanar da cewa Amurka ta mayar da ofishin jakadancinta birnin Kudus daga birnin Tel Aviv. Shi dai birnin Kudus an dade ana kai ruwa rana a kan mallakarsa. Musulmin duniya na kallon birnin a matsayin […]
Kungiyar Hamas ta ce Shugaban Amurka Donald Trump ya kunna wutar rikici ne kawai tsakanin kasashen Larabawa bayan day a sanar da cewa Amurka ta mayar da ofishin jakadancinta birnin Kudus daga birnin Tel Aviv.
Shi dai birnin Kudus an dade ana kai ruwa rana a kan mallakarsa. Musulmin duniya na kallon birnin a matsayin birni mai tsarki domin a nan ne Masallacin Kudus inda Annabi Isa ya yi rayu yake, suma Kirista suna girmama birnin domin a nan ne aka haifi Yesu Almasihu, sannan kuma Yahudawa suna birnin.
Tun bayan kafa Isra’ila, shekaru aru-aru, an rasa wanda zai iya ayyana birnin na Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, duk kuwa da cewa dukan ‘yan kasar suna bukatar hakan saboda tunanin rikicin da hakan zai haifar.
Sai kwatsam, Trump ya ayyana cewa sun amince da birnin ya zama babban birnin Isra’ila. Inda ya ce wannan matakin zai taimaka wajen yin sulhu a yankin na Larabawa.