Trump zai hana amfani da na’urar kara wa bindiga karfi

Shugaba Donald Trump ya yi alkawarin daukar matakan kawar da na’urori da ke baiwa bindigogi damar yin jerin harbe-harbe a cikin kankanin lokaci. An bai wa Jami’ai a hukumar shari’a izinin kafa dokar da za ta haramta amfani da na’urorin wadanda a ka yi amfani da su wajen hallaka mutum 58 a Las begas a […]

Trump zai hana amfani da na’urar kara wa bindiga karfi

Shugaba Donald Trump ya yi alkawarin daukar matakan kawar da na’urori da ke baiwa bindigogi damar yin jerin harbe-harbe a cikin kankanin lokaci.

An bai wa Jami’ai a hukumar shari’a izinin kafa dokar da za ta haramta amfani da na’urorin wadanda a ka yi amfani da su wajen hallaka mutum 58 a Las begas a watan Oktobar bara kamar yadda BBC ta ruwaito.

A baya an sha yin muhawara kan ko hukumomin gwamnati na da damar haramta amfani da wannan na’ura. Amma a yanzu Shugaba Trump ya ba su izinin yin hakan.

Mista Trump dai ya fuskanci matsin lamba tun bayan da a ka yi harbi a wata makaranta a Florida a makon jiya.

Ya kuma nuna cewa zai goyi bayan sabbin ka’idojin kididdige wadanda za su mallaki bindigogi nan gaba.

Read more at http://aminiya.dailytrust.com.ng/news/kasashen-waje/trump-zai-hana-amfani-da-na-urar-kara-wa-bindiga-karfi/31635.html#IZXbHz8GG7xGOggT.99