Trump zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 700 a gidan yari

Ya zuwa yanzu dai kotunan sun same shi da laifuka 91

Trump zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 700 a gidan yari

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka

Kotunan Amurka sun samu tsohon Shugaban Kasar, Donald Trump, da laifuka 91 da aka tuhume shi da aikatawa inda yake fuskantar barazanar daurin shekara 700.

Wannan ne dai karo na hudu da kotunan kasar ke samun shi da aika laifukan da take zarginsa masu alaka da tayar da rikicin zabe da sauran batutuwa.

Kodayake ba lallai tsohon Shugaban ya kwashe daruruwan shekarun a gidan yari ba, amma a bayyane yake zai fuskanci hukuncin daurin.

Ko a ranar Litinin sai da wata kotun da ke zamanta a Jihar Georgia ta kasar ta sami Trump da wasu mutum 18 da laifukan tayar da tarzoma yayin zabukan kasar a shekara ta 2020.

Hakan dai na zuwa ne bayan tsohon shugaban, wanda aka taba tsigewa har sau biyu lokacin da yake kan mulki, ya fuskanci tuhume-tuhume daga ofishin babban mai shigar da kara na kasar, Jack Smith, a laifin kokarin sauya sakamakon zabe.

Kazalika, a watan Yuli ma an tuhumi Trump laifuka 32 kan laifin fallasa wasu muhimman takardun gwamnati a Jihar Florida, sannan aka tuhume shi da wasu guda shida a watan Agustan da ya gabata.

Sannan a watan Maris ma wata kotu a birnin Manhattan ta same shi da laifuka 34 saboda zargin alaka da wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels, gabanin zaben 2016.

Donald Trump, na jam’iyyar Repub;lican dai ya sha kasa a hannun Joe Biden na Democrat a zaben 2020, inda ya gaza kai bantensa a neman wa’adin mulkinsa na biyu.

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

Zulum ya kaddamar da taron gyara karatun tsangaya a Borno

’Yan bindiga sun sace mutane, sun kashe wasu 2 a Sakkwato