Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine

Trump ya ce za su tattauna batun iyakokin kasa da kuma tashoshin makamashi da dai sauran muhimman batutuwa.

Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shirin tuntuɓar takwaransa na Rasha Vladimir Putin da zummar tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

Trump ya shaida wa manema labarai hakan a cikin jirgin shugaban ƙasa na Airforce One a kan hanyarsa ta zuwa Washington daga Florida cewa yana ƙoƙarin ganin cewa yaƙin ya zo ƙarshe.

Trump ya bayyana cewa an yi aiki sosai a game da kawo ƙarshen wannan rikici a cikin ƙarshen makon da ya gabata.

Trump na ƙoƙarin samun goyon bayan Putin a game da tayin tsagaita wuta na kwanaki 30, wanda Ukraine ta amince da shi a makon jiya.

Kazalika, Trump ya ce za su tattauna batun iyakokin kasa da kuma tashoshin makamashi da dai sauran muhimman batutuwa

Sai dai ana ci gaba da miƙa tayin ne a yayin da dukkannin ɓangarorin ke ci gaba da yi wa juna luguden wuta ta sama, har sai da sojin Rasha suka kusan fatattakar dakarun Ukraine a yankin Kursk.

A ranar Juma’a, Fadar Gwamnatin Rasha, Kremlin ta ce shugaba Putin ya aike da saƙo zuwa ga Trump a game da tsagaita wuta ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, wanda ya ziyarci Moscow, inda yake bayyana aniyar tsagaita wuta amma da taka-tsantsan.