Trump zai yi sadaka da albashinsa na shekara daya
Kakakin fadar gwamnatin Amurka Mista Sean Spicer ya ce Shugaban kasar Donald Trump, zai bayar da sadakar albashinsa na shekara daya da ya kai Dala dubu 400 (kimanin Naira miliyan 180), a karshen shekarar nan. Mista Sean Spicer ya ce Mista Trump ya bukaci ’yan jaridar da ke fadar wadanda ya sha sukarsu, su taimaka […]
Kakakin fadar gwamnatin Amurka Mista Sean Spicer ya ce Shugaban kasar Donald Trump, zai bayar da sadakar albashinsa na shekara daya da ya kai Dala dubu 400 (kimanin Naira miliyan 180), a karshen shekarar nan.
Mista Sean Spicer ya ce Mista Trump ya bukaci ’yan jaridar da ke fadar wadanda ya sha sukarsu, su taimaka masa wajen zabo wadanda suka fi bukatar wannan taimako.
Ya ce, “Shugaban kasa ya bukaci ku taimaka masa wajen lalubo inda ya kamata wannan kudi ya isa. Kuma wannan ne hanyar da za mu bi wajen kauce wa sa idon da ake yi, shi ya sa za mu yi amfani da ’yan jarida.”
A lokacin yakin neman zaben Trump an yi ta rade-radin cewa ba ya bayar da sadaka yadda ya kamata, sai dai ya tsakuri kadan daga cikin abin da ya ke da shi ya bayar, inda a lokacin Mista Trump ya ce ba ya da niyyar karbar ko sisi daga albashinsa.
A dokar Amurka, ba a yarda Shugaban kasa ya sadakar da baki dayan albashinsa ba, dole sai ya rage ko da Dala daya ce da zai amfana da ita. Hakan na nufin Mista Trump zai tsira ne kawai da Dala daya daga cikin albashin nasa.
Mista Trump ya zamo Shugaban Amurka na uku da ya sadakar da albashinsa, inda a baya, tsofaffin shugabanni da suka hada da Herbert Hoober da John F. Kennedy, suka sadakar da albashinsu don tallafa wa ayyukan agaji.