Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji
Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi
Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji.
Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya.
- An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe
- Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta
Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu.
Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma suka yi tafiya za su iya kama tashar a shafinta na intanet a https://trustradio.com.ng ko a manhajar Radio Garden.
Haka kuma za a iya saurarenta shafukan Aminiya da Daily Trust da shafukan sada zumunta.
Da zarar tashar ta kammala gwajin za ta fara watsa ƙayatattun shirye-shirye da labarai tare da rahotanni masu ilimantarwa, faxakarwa tare da nishaɗantarwa.