Tsadar abinci: Rogo ya zama abincin yau da kullum a Jalingo

Tsadar abinci: Rogo ya zama abincin yau da kullum a Jalingo

Tsadar abinci: Rogo ya zama abincin yau da kullum a Jalingo

Dafaffen rogo

Tsadar kayan abinci da ake fuskanta a Jihar Taraba ta tilasta wa mazauna garin Jalingo da wasu sassan jihar cin dafeffen rogo a matsayin abincin yau da kullum.

Binciken da wakilin Aminiya ya gudanar ya gano cewa, akasarin jama’a yanzu suna cin dafeffen rogo a matsayin abinci da rana ko da dare.

Mazauna garin Jalingo da wakilinmu ya zanta da su sun ce, a yanzu rogo ya fi sauran nau’o’in abinci araha sannan ga saukin sarrafawa.

A cewar wani mazaunin garin Jalingo mai suna Baba Wuro, danyen rogo wanda ake kasawa a kasuwa ya fi saukin kudi idan aka kwatanta da masara ko shinkafa ko doya.

Ya ce, magidanci mai mace daya da ’ya’ya uku rogon Naira 100 zai ishe su a matsayin abincin rana ko na dare.

Ya kara da cewa, mafi yawan jama’a suna sayen danyen rogo, su kai gida, a dafa, su ci da iyalinsu ko da kuli-kuli ko babu.

Shi ma wani magidanci mai suna Abubakar Isa ya ce, tsadar kayan abinci kamar shinkafa da masara da taliya ta mayar da rogo abincin yau da kullum domin arharsa.

Ya ce, yakan sayi danyen rogo na Naira 1,500 ya sayi kuli-kuli na Naira 500 ya kai gida a dafa.

Amma in zai sa a dafa shinkafa ko a yi tuwon masara ko a dafa taliya yakan kashe kudi masu yawa.

Abubakar lsa ya ce, a baya ana ganin rogo a matsayin abincin talakawa amma yanzu kusan mai kudi da mara kudi duka suna cin rogo a gidajensu.

Wani magindanci mai suna Lawal Jalingo ya ce, kafin ya soma cin rogo a gidansa yana kashe sama da Naira 3,000 a matsayin kudin abincin rana, amma yanzu yana kashe Naira 1,600 domin abincin rana.

Bincike ya nuna cewa, masu sayar da danyen rogo da wuraren da ake sayar da rogo sun karu a ciki da wajen garin Jalingo, sannan yawan masu tallar dafeffen rogo ya karu a garin na Jalingo.

Wani daga cikin masu sayar da danyen rogo mai suna Musa ya cewa, suna zuwa gonakin rogo ne su sayo daga hannun manoma su dauko, su kawo wuraren da suke sayarwa, su kasa.

ACF ta yi Allah-wadai da harin Sakkwato, ta nemi a yi bincike

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9