Tsadar abinci ta karu zuwa 37.8% a Najeriya
Ta alakanta tsadar kayayyakin da tashin farashin hatsi da doya da rogo da da koko da kayan shayi da sauran kayan abinci
Tsadar kayan abinci a Najeriyata karu ta zuwa kashi 37.77 a shekarar 2024 da muke ciki, a cewar Hukumar Kididdiga ta kasar.
Rahoton da hukumar ta fitar ya bayyana cewa karin da aka samu na farashin kayan abincin ya kai maki 7.13 didan aka kwamatanta da na watan Satumban 2023.
Ta alakanta tsadar kayayyakin da tashin farashin shinkafa da wake da da masara da dawa guinea da doya da rogo da dankali da koko da kayan shayi da sauran kayan abinci .
Hukumar ta ci gaba da cewa tsadar kayayyaki a kasar ta karu zuwa kashi 32.7 cikin 100 a watan Satumbar 2024.
- Malaman Kano sun ba wa mutanen Bormo tallafin kayan miliyan N410
- Gwamnatin Libya ce ta hana Super Eagles sauka a Benghazi —Matukin Jirgi
- An daure su shekara shida kan shiga gidan ’yarsu
Alkaluman sun nuna farashin kyayyaki a kasar sun karu da kashi 0.55 cikin 100 a cikin wata guda bayan a watan Agusta an samu maki 32.15% a watan Agusta.
A Agusta ne aka samu raguwar farasahin kayayya a Najeriya, bayan an shafe watanni 19 farashin yana tashi.
Hukumar ta bayyana cewa karin da aka samu a farashin kayayyaki a Satumban 2024 ya zarce na watan Satumbar 2023 da maki 5.98 cikin 100.