Tsadar aure ta janyo barkewar zanga-zanga a Sakkwato

A cewarsa mutane na girmama abin da suka wahala wajen samunsa.

Tsadar aure ta janyo barkewar zanga-zanga a Sakkwato

Sakkwato

Yayin da wadansu matasa a wasu sassan Najeriya ke zanga-zanga kan tsaro da cin zarafin da ’yan sanda ke yi a kasar nan, wata kungiya a Sakkwato ta yi zanga-zanga ce a titunan birnin kan dimbin kudin da ake kashe wa wajen aure. 

Matasan sun bukaci lallai a soke al’adar nan ta kayan ‘na gani ina so’ a jihar wadda al’adar tana nufin kayan da saurayi zai kai wa gidan budurwar da ya gani yake son ta da aure.

Kayayyakin bisa ga al’ada sun kunshi katan-katan din alawa daban-daban da na taliyar indomie da kiret-kiret din lemon kwalba da katan-katan din biskit da buhunan goro da kuma kudi tsugugu.

Galibi iyalai da aminan ango ne kan kai wadannan kaya zuwa gidan budurwar bisa jerin gwanon babura.

A cewar Malam Mustafa Muhammad, ana bukatar akalla saurayi ya kai tsakanin kiret 10 zuwa 20 na lemun kwalba, ya danganta da karfinsa da na iyalan budurwar.

“Sauran kayayyakin ma haka adadinsu zai kasance; sa’annan sai kudin da ba za su gaza Naira dubu 10 ba a matsayin kyauta ga budurwar.

“Wadansu na kai kayan da ya isa mutum ya fara jari da su a shago.

“Su ma iyalan budurwar za su rama wa kura aniyarta wajen hada abinci na gani-a-fada domin tarbar bakin da suka kawo kayan na-gani- ina so.

“Ko a makon jiya, yata ta fada min cewa ta kashe fiye da Naira dubu 100 wajen hada abincin tarbar bakin da suka kawo kayan na-gani-ina so na ’yarta,” inji shi.

Ya koka cewa hakan na da nasaba da matsalolin da suke faruwa bayan auren.

“Yana haifar da hankoron samun duniya sosai daga dukkan bangarorin biyu.

Idan iyalan budurwar sun shirya abin da bai kai daidai da abin da saurayin ya kawo musu ba; to iyalan angon za su ji ba dadi, haka ma na ita budurwar.

“Hakan na kawo rikici a zamantakewar aure, wanda daga karshe ma a iya rabuwa,” inji shi.

Da take magana da Aminiya, Malama Sa’adatu Illo ta ce a nata tunanin ba ta ga laifin al’adar ba, sakamakon hakan na nuna bayyana soyayya da jin dadi a tsakanin masoya.

“Bana goyon bayan soke al’adar don babu wata illa tattare da hakan sai dai kawai wata alama ce ta nuna jin dadin budurwarka ta yadda ka nemi aurenta,” inji ta.

Ta ce al’adar ba ta cin karo da addini ko al’adunsu ba; mutane ne kawai suka yi wa lamarin mummunar fahimta tunda ba lallai ne sai ka kashe makudan kudi ba.

“Da alawar Naira 50 kacal za ta wadatar don ba bukatar sai ka kai katan-katan idan dai akwai soyayya.”

Sanannen malamin addini a jihar, Sheikh Isa Talata Mafara, ya ce al’adar ba ta ci karo da koyarwar Musulunci ba.

“Ya kamata mutane su fahimci bambancin abin,  na-gani-ina so yana daga cikin al’adunmu; amma sadaki da sigar aure addini ne wadannan, domin bai yiwuwa ka yi aure ba tare da sadaki ba,” inji shi.

Sai dai ya bayar da shawarar kada a soke al’adar saboda a cewarsa mutane na girmama abin da suka wahala wajen samunsa.

“Idan aka mayar da aure da sauki, mutane ba za su mutunta auren ba; saboda suna ganin za su saki matar kuma su sake auren wata cikin sauki,” inji shi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos