Tsadar Awo: Sibil Difens Da Karamar Hukuma sun nemi ’yan kasuwa su sassauta farashi

Kwamandan ya ba su kwanaki uku a kan cewa zai dawo dan tabbatar da ganin sun bi umarnin

Tsadar Awo: Sibil Difens Da Karamar Hukuma sun nemi ’yan kasuwa su sassauta farashi

Kasancewar farashin buhunan abinci ya fara sauki amma ba a ganin hakan a wajen awo, Kwamandan hukumar tsaron farin kaya na Jihar Gombe Muhammad Bello Mu’azu, tare da Shugaban karamar Hukumar Gombe suka kai ziyarar ba-zata Babbar Kasuwar Gombe don ganin an sassauta wa masu awo.

Kwamandan a jawabinsa a layin ’yan Shinkafa ya roke su da su rage farashin mudu kamar yadda aka samu sauki a buhu, kuma su dinga cika mudu.

Bello Mu’azu ya gargade su cewa idan sun sassauta, Allah ma zai sassauta musu, kuma su tabbatar da cewa ba sa awo da mudun da aka tauye shi.

Ya ba su kwanaki uku a kan cewa zai dawo dan tabbatar da ganin sun bi umarnin.

Shi ma Shugaban Karamar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmadu Haruna, ya ce sun ziyarci kasuwar ne don su roki ’yan kasuwa su yi wa masu awo sassauci, kamar yadda aka fara samun sauki su ma talakawa su gani a kasa saboda ana cikin tsadar rayuwa.

Sani Haruna, ya ce zai samu lokaci su yi zama da shugabanin kasuwar don ganin an samar da mudun gwamnati saboda tauye mudu ba alheri ba ne.

A cewarsa, kafin ganawar, zai yi zama da shugabannin kananan hukumomia matsayinsa na shugaban kungiyarsu a jihar don ganin sun aiwatar da hakan a kananan hukumomin nasu domin a samu sauki a ko’ina.

A nasa tsokaci, Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuuwa na Jihar Gombe, Alhaji Uba Abdullahi, yaba wa hukumar Sibil Difens da shugaban karamar hukumar ya yi bisa wannan ziyarar sa ido a kan abubuwan da ake gani ba daidai ba saboda a gyara.

Ya ce tun da jimawa yana shiga kafofin yada labarai yana kira ga ’yan kasuwa da cewa su sassauta wa talakawa musamman a wannan halin da ake ciki na tsanani.

Tawagar ta zaga cikin babbar kasuwar Gombe layin ’yan buhuna da masu nama saboda tauye sikile da kuma layin ’yan kayan gwari da sauransu.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe