Tsadar fetur: Dangote da ’yan kasuwa sun sake sa zare

Ɗangote ya ce a yanzu haka matatarsa na da man da zai ishi Nijeriya na kwana 12, amma ’yan kasuwa na kuka da cewa farashinsa ya yi tsada.

Tsadar fetur: Dangote da ’yan kasuwa sun sake sa zare

Sabuwar taƙaddama ta ɓarke tsakanin dillalan mai da Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, kan zargin da ya yi musu ma ƙin sayen man fetur daga matatarsa.

Ɗangote ta bayyana matatar na da lita 500,000 na man a ƙasa, wanda zai ishi kasar na tsawon kwana 12, babu katsewa, ko da kuwa bai ƙara yin aiki ba. Amma ’yan kasuwa sun ce dole sai ya sayar musu da sauƙi, saboda man nasa ya yi tsada.

Tun da Matatar Ɗangote ta fara tace man fetur ake ta taƙaddama tsakanin kamfanin da jami’an gwamnati da kuma ’yan kasuwa.

’Yan Nijeriya sun yi fatan cewa fara aikin katafariyar matatar zai samar da isasshen mai da kuma sauƙinsa a ƙasar.

Sai dai kuma, murna na neman komawa ciki, domin kuwa duk da fara aikin matatar, maimakon farashin ya sauka, sai tashin gwauron zabi yake yi.

’Yan Nijeriya dai sun bayyana cewa babbar buƙatarsu ita ce sauƙin mai da kuma wadatuwarsa, ba irin wannan rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ba.

Da alama dai tsuguno ba ta ƙare ba, domin kuwa a yayin da Ɗangote ke bugun ƙirji da cewa matatar kaɗai ta isa ta wadatar da Nijeriya da duk man da ake buƙata a ƙasar, ’yan kasuwa sun daga cewa dole sai yi musu saukin farashi kafin su saya.

Bayan ganawar Ɗangote da shugaban ƙasa Bola Tinubu me ya sanar cewa nan gaba matatarsa “za ta fara tace a lita miliyan 30 zuwa 32 a kullum.

“Don haka ina ba da tabbacin cewa za mu iya wadatar da ƙasar nan da duk adadin man da take buƙata.”

Duk da cewa Ɗangote bai bayyana farahsin fetur din nasa ba, amma wasu dillalan mai sun bayyana cewa tsadar mansa ne ya jawo ba a saya a cikin gida.

Wani babban dillalin mai ya bayyana cewa bai daɗe da ya shigo mai daga ƙasar waje kuma ya fi na Ɗangote saukin farashi.

Ya ce, “Da man Ɗangote bai yi tsada ba da za a saya. Na san farashin litarsa N977 ne, amma zan iya shigo da shi daga waje a kan N970.

“Idan na sayo lita miliyan 50 a wurin a wurin, asarar miliyan 350, idan na shigonda shi kuma rararsu zan samu.”

Ɗaya daga cikinsu da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “Ɗangote ɗan kasuwa ne kamar kowannenmu kuma gwamnati ta cire hannunta.

“Idan ka buɗe shago amma ba a zuwa sayen kayan, wa za ka je ka yi wa ƙorafi? Ai kai ya kamata ka yi abin da ya dace.

“Ni ma ina da gidan mai, shi ke nan don masu ababen hawa sun ƙi shan mai a wurina sai in fito ina ƙorafi.”

Shugaba kungiyar dillalan mai ta kasa (IPMAN), Abubakar Maigandi, ya ce har yanzu ba sa iya samun man kai tsaye daga matatar Dangote duk kuwa da umarnin da gwamnati ta bayar na a ba wa ’yan kasuwa su saya kai tsaye daga matatar.

’Yan Nijeriya dai sun ce sun gaji da wannan ce-ce-ku-ce, abin da suke so kawai shi ne mai ya wadatu kuma farashinsa ya yi sauƙi a ƙasar.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025