Tsadar fetur: Kanawa sun koma hawa keke da babur mai caji

Al’ummar Kano sun koma tafiya a ƙasa da hawa keke da babura masu caji sakamakon tsadar fetur

Tsadar fetur: Kanawa sun koma hawa keke da babur mai caji

Al’ummar Jihar Kano sun koma tafiya a ƙasa da hawa kekuna da babura sakamakon tsadar fetur inda farashin lita ke kaiwa N1,150.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an samu raguwar motoci a kan titunan birnin Kano a ranar Lahadi, saɓanin yadda aka saba.

A daya hannun kuma masu tafiya a ƙasa da masu amfani da kekuna da babura da kuma baburan zamani masu amfani da ƙarfin wutar lantarki sun ƙaru.

Wani mazaunin Kano, Sani Isa, ya shaida wa NAN cewa kuɗin mota ya yi tashi gwauron zabo, kuma masu baburan A Daidaita Sahu sun ninka kudin abin hawa, saboda tsadar kuɗin fetur.

Ya bayyana cewa a halin yanzu yakan kashe Naira 1,200 a kan kuɗin abin hawa a kullum.

Sani ya ce saboda haka ya koma amfani da kekeknsa, saboda ya fi masa sauƙi.

Shi kuma wani ɗalibi a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Kano Polytechnic, da ke hawa keke zuwa makarantar, Aminu Ishaq, ya ce keken nasa ya kawo masa sauƙi, saboda iyayensa tsofaffi ne kuma ba za su iya biyan kuɗin mota ba a halin yanzu.

Ya ce ni “babu ruwana da ɓata lokacin jiran A Daidaita Sahu, kuma kullum ba ba makarar zuwa makaranta.

Wani ma’aikacin gwamnati, Muhammad Sadiq, kuma, ya ce yanzu ya koma yin rabin tafiyar da zai yi zuwa wurin aiki a ƙasa, domin rage ƙudin da zai buya zuwa wurin aikinsa.

Ya ce, “idan na taka a kasa na rage nisan tafiyar zuwa wani waje sai in hau A Daidaita Sahu, nakam samu ragin aƙalla N300.

“Tun da ƙara kuɗin fetur wasu masu A Daiɗaita Sahu suka haƙura suƙa sauya sana’a.”

Shi kuma Ali Abdullahi, cewa tsadar mai ta sa ya haƙura da hawa motarsa ya koma babur mai amfani da lantarki saboda ya fi sauƙi.

Ya ce, “motocina biyu amma na daina Hawan su, shi ne na sayar da ɗaya na sayi babur mai amfani da lantarki a kan N900,000 wanda ya fi sauƙin kashe kuɗi.

Wani ɗan kasuwa mai suna Tasi’u Murtala, wanda shi ma ya koma amfani da babur mai amfani da lantarki ya ce, kafin yanzu man N5,000 yake sha a motarsa a kullum.

Ya ce amma yanzu baburin lantarkin da ya saya N750,000 ya fi sauƙin kashe kuɗi da kuma biyan buƙata.

“Idan bitirinsa ya samu cikakken caji yakan yi tafiyar kilomita 60 kafin ya ɗauke, kuma ina amfani da janareta ko wutar gwamnati ko sola in yi cajin,” in ji shi.

Kotu ta kori karar neman hana dalibai sanya hijabi

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya